Part 1
Lumshe Ido yayi sannan ya budesu tar bisa kan wata karamar yarinya dake zanen yar galala ....
Fito yayi da bakinsa a hankali ....da sauri yarinyar ta kallo sama tana murmushi tare tsalle tana daga mashi hannu ...
Iska ya huro mata ...sannan ya daga mata hannu ....itama hannun ta daga mashi ....
Wata tsohuwa ta fito daga wani karamin gida wanda duk unguwar babu talaka sama dasu ....
Meenalle ...Meenalle. ..ta fara kwada kira ....
Yar karamar yarinyar ta juyo da sauri tana bata fuska ...cikin shagwaba tace .....Kai kaka ke kullun sae ki batawa mutun suna ...nasha fada maki Meenal fa ake cewa? ...
tsohuwar tace ...to naji sarkin hakuri zo muje ki sayo mana kwaki ko bakijin yunwa?
Saman benen ta kalla. ..har yanzu yana tsaye ita yake kallo ...daga mashi hannu tayi tare da langwashe kai ...sannan taja hannu tsohuwar suka koma gida ....
Kudin ta karbo sannan ta sako hijab ta fito ...tana zuwa bakin kofa taja birki tare da dafe kirji ....hal ka ban tsoro ...ta fada hakoranta waje ...
Hararanta yayi...ke kuma sarkin tsoro ko ...ya fada yana gyara mata hijab dinta ...
Kai ...aikena fa akayi ...ta fada tana neman cire agogon dake makale a hannunsa ...
Hannunsa ya janye don karta bata mashi...sannan yace ...Me zaki sawo?
Baki ta tabe tana kokarin wucewa sannan tace ...kaini Kaka tace kabar sawo man komae ..wae ku yan yankar kaine ...kuma tace wae kaina zayayi tsada ...
Dariya ya sake a hankali kafin yace mata. ..ni kuma kakata tace man indae mace na yawo to kasa ake rufeta ...ya fada idonsa na kallonta ...
Ido ta waro cike da tsoro ...da gaske Mai kamshi?
Ganin ta tsorota ya saka yace ..eh mana ai bana so a rufeki shiyasa ma nace ki fada man in sawo maki ...
Kamar jira take ya rufe baki tayi saurin mika mashi naira hamsin din da ta gama nannadewa ...
Amsa yayi ..yace me zaa sawo. ..
Kwaki na talatin sae sukari na ashirin ...ta fada a hankali ..
kai ya girgiza kana ya tafi. ..har yayi nisa ta kwala mashi kira...ya juyo. .tace ...Dan Allah kace a maka arha ..kuma kayi sauri kar kaka tace na dade ...
Kai ya daga mata sannan ya tafi ..
Baifi minti goma ba ya dawo rike da manyan ledoji. ..tana hangoshi ta tareshi tana dariya ...
Duka ledojin ya mika mata ya juya ...tayi saurin janyo hannunsa ..to ka tsaya mana na duba inda canji ba sae ka bani ba ...ta fada tana bata rai ..
Dariya ta bashi sossae ..ya dawo suka shiga zauren gidan ...
Zama tayi kasa ta zazzage kayan tsaf ...ido ta waro lokacin da ta daga katon gwangwanin madara ..tace ...Nawa ka sayo wannan ...ta fada tana kallonsa ..
Naira biyar ...ya ce idonsa yana kallon karamin bakinta ...
Uhmm saura arba'in da biyar kenan ta fada ...biscuit ta cigaba da fitowa da chocolate sae ledar cos cos da sugar sae lemuka kala kala ...duk wanda ta daga sae ta tambayeshu kudinsa ...daga wanda zayace biyu biyar sae na biyar ....har ta fito da tiyar garin kwaki ...
Wannan nawa yake? ...
Kura mata ido yayi ..sannan yace ...wannan a shagon wani abokina ya bani su ...
Dariya tayi kana ta maida kayan tana kallonsa ...to bani canjina ...ta fada lokacin da ta gama maida kayan ...
Ido ya waro ...wane irin canji kuma?
Harara ta balla mashi ...sha biyar mana. .ba yanzu mukayi lissafi ba naira Talatin da biyar ka kashe ...
Murmushi yayi ..ya lalubi ajihunsa ...babu ko naira 500 bare kananan canji. ..
dubu daya ya mika mata ...ta make kafada ...ni canjina zaka bani ....ta fada a shagwabe
Dukawa yayi dae dae tsawonta ....kiyi hakuri Meenatou ...banda canji...kinji. ki bari anjima zanyi canji sae na baki ....
aa Ni dae ban yarda ba ....muje a canzo su ...ta fada. .
To naji shiga da kayan sae ki fito muje. ...ya fada idonshi a lumshe ...
Ka gudar man da canji ...tace
Hannunta ya kamo ...baran gudu ba ....ya fada har lokacib idonshi a rufe ...
Shiga gidan tayi tana waigenshi ...aje kayan tayi ta fito da gudu ...kaka nata kiranta. ..amma ce mata tayi ....Kaka Kawata ta mutu ake kiranmu muyi mata addua ....
naji dadin wanan labari
ReplyDelete