SANADIN SO ( episode 2 )


 Kafin Aliyu ya ankara tuni Baban ya kawo mishi duka nan ya had'a su ya dunga duka kamar Allah ya aiko shi, sai da yayi musu lilis tukunna ya ce  " yanzu na fara dukan ku 'yan iska, Allah yasa ku mutu na huta da ganin ku" Da sauri Umma ta runtse idon ta tana rushe wa da kuka jin mummunan kalaman da uban su yake yiwa  'ya'yan ta wanda ba yau ta saba jin su a bakin shi ba.  

 

Yana gama fad'in haka ya fice daga gidan yana fad'a kamar wani ta6a66e, Umma tana jin yana fita ta fito waje da sauri zuwa wurin 'ya'yan nata da suke kwance magashiyan a k'asa suna kukan azabar dukan da aka yi musu.  

 

 

Nan Umma ta rasa me zata yi musu kawai sai ta had'a ruwa mai d'umi ta fara yiwa Suhaima wanka, daman ta d'ora ruwan tun kafin mangarib,  sai da ta gama yi mata wanka ta gasa mata jikin ta, tukunna ta kai ta d'aki ta kwantar da ita, sannan ta dawo wajen Aliyu ta kai shi band'aki tare da ruwan wanka tace  "kayi hak'uri Aliyu na, maza kayi wanka ka gasa jikin ka " Gid'a mata kai kawai ya iya yi, sannan ta fito ta tattara garin kwakin da ya zube ta tsince shi tukunna ta jik'a musu.  

 

Dawo wa d'akin tayi ta tashi Suhaima sanya mata kaya tayi sannan ta zuba mata garin a kofi ta mik'a mata, ai kuwa da sauri ta kar6a ta hau shan shi babu k'akk'auta wa. 

 

Ido Umma ta tsura mata tana kallon kumbararriyar fuskar ta ta zuciyar ta fal tausayin su, tana nan zaune Aliyu ya shigo d'akin dakyar ya iya yin sallah sannan ya zauna, mik'a mishi nashi garin Umma tayi girgiza kanshi yayi yana cewa  "Umma ki  sha kawai na k'oshi " Girgiza kanta ita ma tayi idanun ta fal hawaye tace  "A'a Aliyu ka kar6a kasha idan kana son ganin kwanciyar hankali na " 

 

Bashi da yanda zai yi ya kar6a ya fara sha a nutse, ita ma Umma ta d'auki ragowar tana sha, bankad'a labulen d'akin aka yi tare da shigowa ba sallama, babu wanda ya d'ago kan shi ya kalli kofar saboda sun san wane mai shigo wa d'akin a haka.  

 

Ko kallon su bai yi ba ya shige k'uryar d'akin ya zauna saman gadon tare da bud'e kunshin tsire da gurasar da ya siyo ya hau cin abin shi hankali kwance, tuni d'akin ya d'umame da k'amshin naman da gurasar suka hau had'iyar yawu dukanin su har da Umma.  

 

Abin ka da mai ciki akwai kwad'ayi gashi ba ci ake ba nan ta shiga had'iyar yawu akai akai haka ma Suhaima, kallon Aliyu yake yi zuciyar shi tana zafi na tsanar halayyan mahaifin nashi, tashi tsaye yayi tare da cewa  "Umma zan kwanta sai da safe " Don idan bai fita daga d'akin nan ba zai iya had'iyar zuciya ya mutu saboda tsabar bak'in ciki,  kallon shi Umma tayi tare da cewa  "Allah ya tashe mu lafia " "Amin " Yace tare da fice wa a fusace. 

 

"shege mai zuciyar tsiya da bak'in hali " 

Babu wanda ya tanka mishi har Suhaima bacci ya d'auke ta tana had'iyar yawu na son cin naman, kwantar da ita tayi tare da lullu6e ta da zani saboda lokacin hunturu ne.  

 

Tashi tayi tare da nufar gefen gadon k'arfen nata ta kwanta a can k'arshe tana mai tunanin makomar rayuwar su a gaba, ga cikin ta da yake k'ugin yunwa da haka bacci ya fara d'aukan ta, can cikin baccin nata taji mijin nata na lalubar ta alamar akwai abin da yake nema a wajen ta, wasu hawaye ne masu zafi suka dunga fita a idanun ta, duk dare ta saba da wannan halin mijin nata gashi ba abinci kirki yake basu ba, shi yasa kullum take tashi jiki ba kwari a gala6aice, tana kuka shi kuma yana sha'anin gaban shi har zuwa lokacin da ya rabu da ita ya juya mata baya, ba dad'e wa ta fara jin saukar minsharin shi, dakyar ta iya mik'e wa ta fito zuwa band'aki tayi wanka don bata iya bacci a haka, tana fito wa ta ga Aliyu zaune a tsakiyar gidan ga tsananin sanyin da ake zabga wa cikin mamaki tace  "Aliyu lafiya? " D'ago kanshi yayi tare da cewa "Umma na kasa bacci ne, zuciya ta rad'ad'i take min " Ya k'arasa fad'a hawaye na fita a idon shi, cikin tausayin shi tace  "kayi hak'uri Aliyu komai tsanani yana tare da sauk'i, bana son kana sa damuwa a ran ka wani ciwon ya kama min kai, kasan kai ne mai taimakon mu, yanzu tashi kayi alwala kayi sallah tare da addu'a, ka mik'a wa Allah buk'atun ka " Tana nan tsaye yayi alwala sannan ya shige d'akin shi, tukunna ta juya ta shige d'akin ta kwanta, jikin ta babu k'arfi da ita ma nafilar zata yi ta fad'a wa Allah matsalar ta, amman duk da haka sai da ta janyo carbi ta fara istigifari tare da salatin Annabi (SAW),  da haka bacci mai k'arfi ya d'auke ta........... 

Post a Comment

Merci de laissez vos commentaires.

Previous Post Next Post