Bismillahir Rahmanir Rahim.
"Subhanallahi! Wannan bala'i ya yi yawa, a ce a kwana uku an kashe mutane goma? Masu kama macizai
mutum takwas, wannan wani irin masifa ce ta macizai da ya fara addabar mu haka a gari? abu sai
tsamari yake yi, tun ana samun sara kaÉ—an-kaÉ—an, ga shi saran macizai din bakinsu da girma! Me yake
shirin faruwa ne haka a cikin wannan alƙarya na da mutanen yanki na?" cewar mai garin yankin kauyen
kwana dake jihar yola da yake can cikin dajin fulani wanda ya cika da albarkatun korayen shuke-shuke, a
wannan sassanin fulani ne suke rayuwa a wannan yanki, kuma su na da yawa dan sun hayayyafa, basu
fita cikin gari kuma ba a shigo musu.
Jama'ar da suke tsaye a wajen ne cike da jimami da fargaba su na alhini, wani dattijon tsoho cikin
harshen fullanci ya ce
"Gaskiya muna cikin hatsari a wannan alƙarya, ga shi yanzu an fara samu kisan macizai da yawa, ya
kamata mu san abun yi" sai tattaunawa suke yi ta yadda zasu shawo kan wannan babbar matsalar da
suke ciki, wata kyakkyawar budurwa ce a tsaye a can gefe fara sol, tana da idanun mage, sanye take da
kayan fulani ta naÉ—a farin mayafi a saman kanta, ta rufe gefen fuskarta da shi, rabin gashinta ya sauko ya
rufe mata rabin fuska wanda ya sake hana asalin kyawun nata fitowa sosai a gani,kafarta babu takalmi, a
hankali ta bi mai kama macizai wanda aka kashe da kallo, ranta a b'ace ta juya a hankali tana tafiya
dukkan sassan jikinta yana lankwasawa, a yadda take taka kasa da ka ganta kasan bata yi maka kama da
cikakkiyar mutum ba, daji ta yanka ta shiga cikin korayen bishiyoyi inda zata samu yar uwarta kawai take
hari, can kusa da wani rafi mai sanyi da dadin kallo ruwan fari k'al da shi abun sha'awa taja ta tsaya, bata
ankara ba taji saukan wani zureriyar wutsiyar maciji, ko kaÉ—an hakan bai tsoratata ba, tunda ita ma
macijiyar ce, d'aga idonta ta yi saman bishiyar da wutsiyar macijin ya sauko mata, ta kalli yar uwarta
wanda dukkanta macijiya ce,a hasale ta ce
" AZIMA!!? me yasa kika son kashe mutane kwanan nan ne kam?" macijiyar da aka kira da Azima a
hankali ta sulalo daga saman bishiya ta kanannaÉ—e yar uwarta tana lasarta da harshe, hannu dayar tasa
ta ture kanta a macijiyar, sannan ta ce
"Azima tambayarki fa nake yi?" gefe ta koma ya yinda ta saki wani huci ta girgije nan ta zama rabi
mutum rabi macijiya, daga ƙugunta abun da ya yi sama mutum ce, daga kugunta abun da ya yi ƙasa
macijiya ce.
Dariya ta sheƙe da shi cikin wata murya mai amo da rashin dadin sauraro, sai jijjiga take yi tana naɗe
jelar macijinta ta ce
" AZIZA! bana mantuwa kuma bana yafiya!! Duk wanda ya shiga gonata sai na hallaka shi, sai na ga
bayansa ko ma waye! Duk wanda nake kashewa sun tab'oni ne! Dan haka bana bukata ki din ga
tuhumata akan abun da kike da masaniya a kai"
"Amma Azima kisan ya yi yawa! Da an miki laifi kaɗan sai kisa? So kike yi sai an gano mu ba mutane bane macizai ne mu a kore mu a gari?" Rintse blue eyes dinta Azima ta yi sannan ta buɗe tana zaro harshenta suffan na macizai sak ta ce "Ina so na bar wannan alk'aryan, ina so na shiga cikin gari wanda yake da al'umma da yawa ta yadda zan tarwatsa su!" girgiza kai Aziza ta yi ta ce "Ke nan za ki iya tafiya ki bar su Baffa da Hajja?" "Me zai hana Aziza!? Ina da burin shiga cikin jama'a masu yawa duk da na san ni din ba mutum ba ce!" "Shigarki jama'a ba alkhairi bane Azima, dan haka ki bar wannan maganar ki zo mu tafi gida kar mu koma mu samu Baffa ya dawo ya titsiye mu da tambaya daga ina muke, amma dan Allah ki koma mutum tun daga nan" Aziza ta faɗa tana yin gaba, dariya Azima ta yi a madadin ta zama mutum kamar yadda aka ce mata sai ta rikiɗe ta zama katuwar macijiya mai sheƙi da ban tsoro, ko da Aziza ta juya ta ganta a haka girgiza kai ta yi, ba tare da ta ce mata uffan ba. Sai da suka kusan isowa gida kafin ta girgije ta zama mutum, yadda yar uwarta Aziza ke tafiya haka ita ma take tafiya, mayafinta da ta ajiye ne kusa da gida ta dauka ta yi irin lullub'in da yar uwarta ta yi, su na yin wannan lullub'i ne saboda idanunsu da yake abun tsoro barin ma kwayar idon Azima blue, ita kuma Aziza idon mage mai fari-fari, ko kaɗan basu da baƙin ido,shi yasa Hajja mahaifiyarsu ta basu su din ga lullubi, shi yasa idan sun yi lullubin suke saukowa da dogon gashinsu ta gefe ya rufe musu gefen fuska, ga shi dai alk'aryan duk fulani ne kuma kyawawa, amma duk fadin yankin kwana babu mace ko namijin da ya kai su AZIMA DA AZIZA kyau. Ko sallama basu yi ba suka shiga gidan suka iske mahaifiyarsu Hajja a jikin murhu tana aikin hura kara, Aziza ta ce "Sannu da aiki Hajja" dagowa ta yi ta kalli kyawawan yan biyun nata ta ce "Yauwa sannu Aziza, daga ina ku ke haka? Tun safe fa ku ka fice a gidan nan" "Amm Hajja muna rafin jimulo" murmushi Hajja ta yi ta kalli Azima wanda idonta yake kan garin Mahaifiyarta, haka kawai take ji ta watsawa garin dafi, Aziza ta ce "Hajja karan ya ƙi kamawa ne?" "Eh Aziza ya ƙi kamawa wallahi ga idona ya yi ja yana min zafi" "Ayya sannu Hajja bari na hura miki!"