Part 1
Ummi tana tafe tana yan wakokinta, tareda gudu
hade da tsalle. cinikin ummi ne gudu, sam bata
tafiya a hankali.daga can gefe ta hango wata
yarinya wadda bazata wuce sa'arta ba.
tace,"yauwa,ga firdausin data tsokane ni" ta nufi
wurinta ,tasha gabanta ta rike kugu. "fiddausi wa
kike tsokana? fiddausi tace "ban tsokane ki ba
fa".cikin tsoro tayi maganar .ummi ta shako mata
wuya. ina jin lokacin da kika ce ummi tsiga.ban
ce ba inji fiddausi .ummi ta hankada ta tare da
cewa "Allah yaso ki." nikan garin da fiddausin tayi
ya tarwatse a kasa tace "kin gani ko? wallahi sai
kin biyani"ta soma kuka,ummi ta sheka da
gudu,sai gida. tana ajiye man gyadan data siyo ta
nufi ba daki don fitsari ya matse ta .umma dake
zaune tana fadin. "da mutum!da mutum!!" saida
ummi ta bude . Ganin yaya Abba tayi,da gudu ta
juyo ta fada dakin umma,jiki na bari bayan tayi
bol da dakakken yajin da umma ta daka zata
soya mai don cin abincin rana. sai kuma ta tuna
cewa bata tsira ba,don Abba tsaf zai binciko ta.ta
fito da gudu ta nufi dakin tsohuwa. tsohuwar tana
sallar azahar.ummi ta tsallake ta ta kutsa kasan
gado.nan ma tayi ciki da furar da tsohuwar keson
sha da zarar ta idar da sallah. Alhaji babba tasa
ya aiko mata da furar daga kasuwa.don tasha da
rana. Abba ya fito wanka ranshi a bace.dakin
umma ya nufa yana fadin "ummi ke ummi zonan"
Ya samu Umma tana tattara yajin da Ummi ta
zubar, tana fada. Ya ce, "Umma ban san irin
dukan da zan wa Ummi ba yau. Ta ce,"Abba ka
mata dukan mutuwa, na gaji da halin Ummi.
Yarinya sai ka ce 'yar fata? Ka dubata ta tafi
dakin Tsohuwa, don ta san zata hana a dake ta."
Ya ce,"Allah sai dai Tsohuwa ta yi ta fadanta,
amma ba zan barta ba. Ya juya zai tafi, suka ji
muryar Tsohuwa tana fadin. Ba zan yi fada ba, ka
kashe ta ka ji mai sunan Malam, ba na son ka
barta da rai. Ta dubi Umma" ke kuma Suwaiba
dama kin san ba za ki daraja sunana ba ki ka sa
a ka sa miki don kiji dadin ci min fuska?" Umma
ta ce," Ba haka ba ne Tsohuwa, Ummi ba ta yo
halinki ba. Ita fa rashin hankali ne da ita. Yayanta
fa ke wanka ta zo ta leka shi, nan kuma tazo ta
zubar min da barkono. Abba ya ce, "Umma don
Allah kiyi shiru ki kyale Tsohuwar nan, ai ita ta
6ata Ummin, duk abn da yarinyar nan tayi sai ta
hana a yi mata fada. Uhm duk fadanki yau sai na
dake ta, ba sunan ki ba in ma kece,"Tsohuwa
tasa kuka gami da salati. "Yanzu mai sunan
Malam ni ka ke fadawa haka?" ya ce, "An fada
miki." Umma ta ce, "kai Abba zan sa6a maka
jeka." Ta juyo wurin Tsohuwa, Don Allah kiyi
hakuri............... Maman Fiddausi ce tayi sallama
tare da Fiddausin suka shigo. Ran Maman
Fiddausin a 6ace, ta tsaya rike da gari a
hannunta ta dubi Umma. Ta ce, Umman Abba
dubi abn da Umminki tayi min don Allah, yarinyar
nan tayo nika da kyar," tun safe sai yanzu na
samu, amma ta zubar min." Abba ya ce, Kinga
halinta ko?" Tsohuwa ta ce, "Wannan ba matar
Bala ba ce?" Maman Fiddausi ta ce, "Ni ce." Ta
ce," To kije kije ki nemi wanda ya zubar da
garinki, Ummi ko fita ba tayi ba. Umma ta ce, "
Ta fita Tsohuwa, na aike ta siyan mai." Tsohuwa
ta ce," Tsokanarta a ka yi to. Umma ta amshe
abin garin ta zuba musu, sannan ta ce, "Don
Allah Tine kiyi hkr." Abba ya nufi daki. Sai da ya
shirya tsaf, sannan ya dauki belt ya nufi cikin
gida, dakin Tsohuwa ya shiga kai-tsaye kasan
gado ya nufa. Ya jawo ta, ta soma kurma ihu.
Daya ya lafta mata amma ta dane shi tare da
cukwikuye belt din tana ihu. Tsohuwa ta iso tana
dukanshi a baya, fadi take "Za ka kasheta ne?
Jama"a kuyo dauki. Haushin hakan yasa shi
damko kanta ya shiga zuba mata kola, ya
sirmiyota ya shiga lafta da takalminshi, tunda ta
hana belt din. Sai da ya mata tas, sannan ya fita
ya bar su, Tsohuwa na kuka Ummi na kuka. , Sai
da komai ya natsa ta leka ta jawo furarta don
tasha, sai ta ganta a zube. Ta ce, A" a ke ki ka
zubar min da fura?" Ummi ta ce, To ba shi ne
janyo ni ba Yaa Abban. Tsohuwa ta ce, "Ai ko sai
ya siyo min furata. Ta mike ta wuce Umma tana
rabon abinci, ta nufi soro in da dakin Abba yake
(Zaure) Ya fito yana rufe kofa, ta ce "Au za ka
fita ba? To ka sawo min furata da ka zubar. Ko
kallonta bai yi ba ya rufe kofarshi ya wuce. Ta ce
mishi "Aikin bana, in ba siyo min ba ubanka ai ya
dawo ko min dare ya sito min. Abba ya ce, Ku ku
ka sani. Ra ce, kaima ka sani, dan jakar uba. Ta
dawo ciki tana mitar ya cika bakin rai. Umma ta
ce, "Ina Abban? Tsohuwa ta ce, "Ya tafi, in bai
sai min furata ba ranshi zai 6aci yau a gidannan.
Umma ta ce "Ni bai ma ci abinci ba ya fita, ke
Ummi zo ki kira min shi, yunwa fa yake ji.
Tsohuwa ta ce, "Ba za ta kira shi ba, ya dake ta
sannan ta kira shi? Tunda bai barta taci da dadin
rai ba, shi ma ba ya ci ba.,, Umma tayi shiry,sai
haushin Ummi da take ji kamar ta shake ta ta
mutu. Ummi tayi wanka ta zura kayan Mkrnt,
tana saka sandal Umma ta ce, "Ina Ummi? Zo
nan." Ummi ta tafi tana cewa a ranta. "ALLAH
YASA DAKIN YAYA ABBA ZA TA AIKE NI, SAI NA
RAMA DUKAN DA YA YI MIN JIYA, DON YANZUN
DUK ME YA MIN SAI NA RAMA.........." Umma ta
katse mata tunani da cewa,"dauki shayin Abba ki
kai masa kada yayi latti,kai shayin ki dawo ki
dauki dankalin,yau shi kadai ma nayiwa dankalin."
Tace,"nifa?"umma tace "ke kina cin dumame
Abba ko ba ya ci,dan haka dan wanda ya rage
shi nayi wa." Ummi ta figi kayan tea din ta nufi
dakin Abba tana tura baki.tare da sallama bata
jira amsa ba,ta daga labule ta fada. Dabi'ar da
yake mata fada akai kullum,ya gama saka
singiletinshi kenan yana kokarin saka riga. Yace,
"wai ke wace irin majanuniya ce?ban ce miki in
kinyi sallama sallama sai na amsa za ki shigo
ba? sai kawai ta saki tiren,ruwan zafin ya zube
masa a kafa,dankalin ya watse kan rigar da zai
saka. tayo waje da gudu,sai dakin tsohuwa.ya
fito da sauri yana cewa,"umma ta kona ni! ta
kona ni!!" da sauri umma ta fito daga dakin Alhaji
babba,shima Alhajin na biye da ita yana fadin
"wacece ta kona ka?" Yace "ummi ce! ummi
ce!!."nan take Alhaji babba ya rike kafar yana tofa
mishi addu'a. Umma ta debo kullun kamu ta zuba
mishi,amma duk da haka sai da yan yatsun
kafarsa suka kumbura. tsohuwa ta fito daga daki
tana fadin,"kai ummi bata ji? wai ni meyasa aka
sa mata sunana?" Abba ya kalli tsohuwa cikin
takaici yace,"duk ba ke kike daure mata gindi ba?"
Umma ta shiga dakin tsohuwa ta janye kayan da
tsohuwa ta jera don kada aga ummi,ta janyota
tun daga dakin take kwallo da ummi har waje.
Alhaji ma yau har dashi aka zane ummi,tsohuwa
dai sai yan mitoci take yi,wai yanxu haka ma
bata sani bane. Abba dai ranar dai bai je
makaranta ba,haka nan da yamma sai da ya saka
ummi a dakinshi ya bata gwale-gwale sannan ya
zane ta. misalin hudu da rabi na yamma,Ahmad
abokin Abba yayi sallama a kofar gidan,Abba ya
amsa ya fito. Suna zaune kan dakalin kofar gidan
suna hira,sai ga ummi ta yanko da gudu tana
waiwayen baya. Ya ce,"zo nan."tazo yace,"kinyo
tsokanar fada ko?" tace,"a'a.yace in har tsokana
ki kayo zaki sani shegiya mummuna kazama. Ta
murguda baki,yasa takalmi ya jefeta,ta shige gida
sai ko ga wani yaro jiki duk kwata yayyanshi na
biye dashi. ya tambayesu,suka ce "ummi ce ta
jefa shi kwata"ya taso yaron har cikin gida ya
kamota dakin tsohuwa ya tsareta ta wanke ma
yaron jiki,ta kuma wanke kayan. sannan ya
zuzzuba mata kola a kai.tsohuwa tana ta yiwa
yaran fada,wai ita ma su daina tsokanarta Umma
ko lekowa bata yi ba,ya fito ya samu Ahmad yana
cewa "kayi hakuri na barka kai kadai." Ahmad
yace,"ba komai" sai Abba ya zauna sannan
Ahmad ya dube shi. Abba wannan kanwar taka
kuwa bata da Aljanu? Abba yace,"ba kowa
akanta,sai iskanci." Ahmad yace."a'a,kai dai ku
kaita ayi mata rukiyya." Abba yayi dariya,sannan
yace kasan Allah ba kowa akan ummi,saboda
Alhaji karami ya taba yin wannan tunanin. ya
dauke ta yakai ta rukiya bata da komai."Ahmad
yace tabdi!,gaskiya in ta isa aure duk wanda ya
aureta akwai aiki babba a tare dashi. Abba ya
ce,"wane mahaukaci ne ma zaya dibar ma kansa
ummi?"Ahmad ya ce,"sai ai muku hadin ggida..."
ya kaima Ahmad naushi a gefen ciki,Ahmad ya
kauce yana masa dariya. Abba ya ce,"ka cuce
ni,ace in auri ummi ai sai na hada kayana na bar
garin nan. nan. Ahmad ya s heke da dariya har
da rike ciki.sannan ya ce,"don me? Abba ya
ce,"to wannan yarinyar ba sai ta hada maka
gobara gida ba?gata kazama ga muni." Ahmad ya
ce,"kama dai kuke yi." Abba ya bata rai,"Ahmad
bana so.in har da gaske ina kamada ummi ba sai
na koma ciki an sake haifana ba. Don Allah ni
tashi ma ka tafi,don wallahi da don kai bane kake
fada min haka da sai munyi rigima,na tsani
ummi,bana sonta sam! Zaune suke a kofar gidan
Alhaji babba kan katuwar tabarma,sun jere abinci
suna ci. kullum Alhaji babba da Alhaji karami nan
suke zama tamkar tagwaye,suna matukar kama.
mafi yawancin lokuta ma kaya iri daya suke
sakawa,domin Alhaji babba duk kayan daya saya
tare yake sai musu. haka nan hula ko
takalmi,haka nan matansu baya
bambantawa.shima Alhaji karami duk da bai kai
samun babba ba yana koyi dashi. Alhaji babba ya
kalli karami yace,"Aminu ya zancen makarantar
bashir?" Alhaji karami ya dubi wansa ya ce,"Alhaji
bashi fa ya fadi jarabawa,jiya na tsare shi da
maganar sakamakon jarabawarshi yace bai duba
ba,saida yaji nace zan hada shi da Abba suje
sannan yace min yaje wai duk ya fadi. Alhaji
babba yace,"Ash sha! sai ya maimata shekara
kenan?"Alhaji karami ya ce,"to in ma ba zai
maimaita ba Alhaji shi ya sani,ba sahura ta bata
su ba? shi Abba ai ba haka yayi ba,ka dubi fa
yadda yaki aikin kanikancin nan,uwarshi ta zuga
shi wai yayi karatu kadai yayi aikin gwamnati.
kullum haka sahura take kitsa ma yaran."Alhaji
babba yayi yar dariyar takaici,sannan yace"in
banda abin sahura yadda kasan nan tamu ta
zama waye zaici alwashin aikin gwamnati? ina ce
masu digree ne ke yawo ba aiki?" "har masu
masters." inji Alhaji karami.ya tashi zaune daga
kishingidar da yayi,yace dubi misalin dan
abokinnan naka Alhaji buhari." Alhaji babba ya
ce,"kwarai kuwa,mas'ud ba.yanxu ma fa kasuwa
yake zuwa,sai yanxun yake koyon kasuwancin."
Alhaji karami ya ce,"to daya dora shi a kasuwar
fa tun farko?shi yasa na fada ma sahura ta bar
yara su hada da sana'ar hannu. Donni dai yaro
kamar bashir yanxun ba zan dauki kudina in ba
shi ba."Alhaji babba yace,"shi yasa kulum nake
kara son Abba,yaron nan da kanshi yace min in
kai shi shagon dinki. Har naki suwaiba ta
ce,"Alhaji ka kai shi in ya iya sana'ar hannu ko
bai samu aikin gwamnati ba zai rike kanshi da
sana'ar nan." Alhaji karami ya ce,"to ai kasan ita
suwaiba tasan abinda take yi.amma sahura sai
addu'a." Sallamar Abba ce ta katse su,ya zauna
can gefe sannan ya gaishe su,duk suka amsa tare
da tara hankulasu gurinshi. Ya mika ma Alhaji
babba kullin takarda tare da cewa "Alhaji gashi
maganin (ulser)ne" Alhaji babba ya amsa ya
ce,"Abba sarkin amsa magani, a gurin wa ka
samo wannan kuma?" ya ce,"Ahmad abokina na
raka ya amso ma babanshi,shine nace bari in
amso muku" yace to Allah ya saka da
alkairi."Alhajikarami yace"dame ake sha?" Abba
ya ce,"da madara peak." suka ce"to" daya mike
zai shiga gida Alhaji babba yace ya shige da
kwanikan abincin. yau kam Abba bacci yake ji da
wuri,don haka ya baro shagon dinkinsu wanda ya
kan kai goman dare a ciki ya nufo gida. Ya bude
dakinshi ya shiga ya cire riga sai singileti da
gajeren wando na jeans.ya nufi ciki don ya kama
ruwa ya kuma yi wa ummanshi sallama. tsakar
gida ya sameta zaune ta zabga tagumi,inda
abinda Abba ya tsana shine,yaga ummanshi cikin
damuwa. da sauri ya isa wurinta,"umma
lafiya?"ta dube shi "ina fa lafiya,ummi ce tunda
tayi sallar isha'i ta fice kusan awa guda zance
jiya ka mata dukan fita wasan dare?" Abba yace
"to wai me za'a yi wa ummi ne ta zama irin
sauran yara?" umma tace,"addu'a ce Abba,kuma
muna yi kullum." ya juya cikin bacin rai,layin su
Amina kawarta ya nufa,don bata wuce can.duk da
cewa Amina bata kaita rashin ji ba. can din kuwa
ya sameta,ta tara zugan yayan layi sai tsokanar
fada suke yi,ita ce shugaba. wata falwaya Abba
ya samu ya jingina yana kallonsu,don yana iya
tunkararta su diba da gudu. shi kam ba za ya iya
guje-gujen nan ba,duk wanda yazo wucewa sai
sun tsokane shi,wani su jefe shi,wani kasa zasu
watsa masa su gudu wani kuma rigarsa zasu ja.
c can wani shida budurwarsa sun zo wucewa ta
fizge ledar hannunsu ta watsar,sannan suka ruga
da gudu. tayo gurin da Abba ke tsaye bata zaci
da mutum a gurin ba,sai dai taji anyi caraf da
ita.sai da Abba ya zabga mata koso a tsakiyar
kai har tayi fitsarin wuya,sannan ya tasata har
gurin mutumin data yaga ma ledar. suna
tsugunne suna tsintar lemunsu da ayaba ya
ce,"malam ga wadda ta yaga muku leda." da
zafin nama mutumin ya mike,Abba ya
ce,"gata"mutumin ya shakota yace yau sai naga
ubanki." Abba ya ce,"ko kara ka kai gidansu nine
zan hukuntata,don haka gata na kawo maka
kanwata ce kuma naga lokacin data tsokaneka."
jikin mutumin yayi sanyi ya ce,"na gode bawan
Allah,taje taci albarkacinka." Abba yace "daka
nade ta." mutumin yace,"ba komai,ke kuma ki
canza hali ke mace ce." Abba yace nagode"
sannan ya tasa ta zuwa gida. Bokiti ya cika da
ruwa ya dora mata,,umma rasa bakin magana
tayi daya sanar da ita tsokanar daya tarar da
ummi suna yi. Daga karshe ta ce,"Allah ya
shiryaki,abind ya sameki kada ya sami sauran
dangi. Alhaji kuwa daya sameta dauke da bokitin
tana kuka tana fadin "yaya Abba na tuba,bazan
sake ba." ya ce,"uwata bakya ji ne fatan Allah
yashirye ki."ya nufi dakinshi.tsohuwa takaicin
Abba ne ya hanata fitowa tayi magana. nata
ganin,ummi bata wuce fita tayi wasa da
kawayenta ba,a cewarta ba laifi ba ne. amma an
bi an tsangwami yarinya,an hanata walawa.sai da
Abba ya gaji dan kanshi sannan ya sauke mata
ruwan. Sannan ya mammaka mata
takalmi,sannan ta shige dakin
tsohuwa.tsohuwana daga kwance ta dubeta.
"yaga dama ya kyaleki?kai mai sunan malam
akwai mugunta.zo ki kwanta." cikin kuka ummi
tace,"kayana sun jike,bokitin ruwa fa ya dora
min."tsohuwa tace,"barshi da halinsa,ace mutum
ba zai sake ba?" ummi tace,"ai sai na rama,shima
din sai yayi kuka."tsohuwa ta ce,"a'a,kada ki
soma zancen ramakon nan.kin san ko kin rama
ke ce zaki kwan ciki." ummi ta ce,nifa sai na
rama."tsohuwa ta ce,"baki gaji da shan wahala
ba kema da shegiyar gaddama,ga zanina nan
kikin raki ciro ki daura kizo ki kwanta." ummi tayi
lamo bayan tsohuwa tana tunanin dame zata
rama abinda Abba yayi mata jiya.har bacci yayi
gaba da ita waiwaye............. SULAIMAN shine
asalin sunan Alhaji babba,Aminu kuma shine
Alhaji karami. tsohuwa itace mahaifiyar su,kuma
su kadai ne yayan data haifa.Asalinsu yan
zamfara ne a kauyen daji a karamar hukumar
kauran-namoda. malam Idris mahaifinsu shine ke
zuwa yawon fatauci,har Allah ya zaunar dashi a
garin kano,da matarshi Habiba. sunzo da
yayansu guda biyu,sulaiman da Aminu.sun yi
karatun muhammadiyya mai zurfi,amma basuyi
karatun boko ba. sannan ya dora sukan harkar
kasuwanci,Allahya albarkaci kasuwancin Sulaiman
inda harkoki suka bude mishi cikin kankanin
lokaci. matsalar shi daya rashin boko,malam
idrisu mahaifinsu yana daya daga cikin wadanda
basu amshi boko ba lokacin da tazo. Don haka
sam bai saka yayansa ba.Sulaiman ya auri
Suwaiba wadda suka dauki watanni suna
soyayya,ita yar unguwar sheka makaranta ce.
Amma asalinsu yan Daura ne jihar Katsina.kafin
aurensu sai da yayi gini a unguwa uku gidaje
guda biyu iri daya. Ya ce Aminu kaninsa ya zabi
gida duk da cewa a lokacin baiyi auren
ba,wannan abu yayi wa mahaifisu dadi. yayi ta
shiwa Sulaiman albarka,don haka sai aka rufe na
Aminu,yayin da sulaiman ya tare a nasa da
matarsa Suwaiba.
ZURFIN CIKI
Part 2
Marubuci : Abdul Nassir @AbdulNetwork
Kwanci tashi 5yrs ta miqa suwaiba bata taba ko
batan wata ba. awannan yr ne mahaifinsu ya
cimma 1yr da rasuwa. saida aka watse makoki
danginsu na qauran-namoda suka koma. sannan
sulaiman yace da aminu, to ni xan dauki tsohuwa
in maida ta gidana,kai kuma aminu ka fito da
mata kayi aurenka dan mu xauna kusa da juna.
tsohuwa ta saka kuka tace wannan yaran nidai
da ka barni na xauna da gidan xai xama kufai.
sulaiman yace tsohuwa kiyi haquri, sai a saka
haya.aminu yace haka xa ayi. daqar tsohuwa ta
yarda dan tace ita wannan gidan mutuwane xata
rabata dashi, dan gidane me tsohon tarihi a
gurinta. ta ce gidan da mijinta ya rasu gidan da
ya kawo ta tun tanada jajayen sawunta. suka dai
lallabata. lkcn da aminu ya gabatar da sahura a
matsayin matan da xai aura, tsohuwa ta tuma ta
ce ba ta laminta ba, don kuwa kowa yasan
mahaifiyar sahura gun masifa. sanna sahurace ta
gajeta. aminu sai ya watsar da mgnn auran
gabaki daya har tsawan lkc. sulaiman yanata
roqan tsohuwa ta amince, dan ya lura aminu yayi
nisa. Ba yadda tsohuwa ta iya, dole ta amince,
aka sha biki ta tare gidan aminu. mai hali dai
baya fasawa, dan sahura batasan hulda da
suwaiba da surukarta, gashi daga kawota ko
2mth bata yiba ta kama fada da yan unguwa. a
cikin 3yrs sahura aka samu ciki. lkcn sulaiman ya
samu xiyarta qasa mai tsarki shida tsohuwa dan
sauke farali. sunyi addu'a allah ya bashi xuri'a
shida aminu.suna durowa gida suka samu lbrn
cikin sahura, murna a gun sulaiman tamkar
matanshi ne keda cikin.lkcn haihuwa tahaifi da
namiji murna gun yan uwa biyu ba'a magana,
anyi shagalin suna inda yaro yaci sunnan mahai
finsu wato idris shine suke kiranshi abba. Sannan
Ahaji Sulaiman ya biyama qaninshi kugeran
makka daga nan ne aka samu ahj Babba da ahj
qarami tun abba yana jariri ahj babba da
matanshi suke dawainiya dashi Sahura ba taso
saidai ba yan da xaitai da ita. domin alj qarami
na gama shirin fita xai saba shi sai gidan sai yayi
kukan nono ake maida shi, saidai tayi ta mitar
cewa anriqe mata yaro gidan,sahura dai in an
kawoshi bata isa taxoba dan tasan tsohuwa
tafita danja.duk da gugar xana da haibaici da
sahura take antayo ma suwaiba ta katanga ko
inta je gidan, baisa ta daina dawainiya da abba
ba. cikin hakane sahura wata ran sahura ta tashi
da xaxxabi mai tsanani da amai, shine taje asibiti
ganin likita ya tabbatar mata da tana dauke da
ciki.ko da ta fadama alj qarami ba qaramin murra
yayi ba ita kuma ta batarai, yace tunda abba
yana tafiyan shi ko ina ayaye shi. Da yamma
bayan yadawo kasuwa ya shiga gaida tsohuwa
shine yake gayamata xa'a yaye abba. tace
saboda me? ku barshi yayi 2yrs. sai yace ai uwan
tanada juna biyune, shi yasa, daman sha waran
da nakesan fada maki shine xanba yaya shi
kyauta har abada.tsohuwa tace kai amma ka
kyauta. Washegari da safe shine ma yayi ma
abba wanka tana kwance ya shirya shi, sannan
yace mata ta hada kayanshi duka dan xan kaishi
gidan ahj babba gaba daya. tace kana nufin kayi
kyauta dashi gaba daya? yace ea. tace tabdi!,ba
xai yiwu ba. infishari banxane kaxa tayi mana. su
wa yace kada su dage su samu nasu dan? nima
wahala nasha na haifi dan, ba shago na bude ya
fito ba....sam bai kulata ba, ya hada kayan yaran
ya fita. ya shiga gidan ahj babba da shi. dakin
tsohuwa ya shiga, nan ya samu ahj babba suna
gaisawa, yace yauwa, dama gurinka naxo yaya.
abba ya sauka daga jikin babansa yaje jikin ahj
babba da gudu, ahj ya dauke shi ya rungume. Ahj
qarami ya keqa ya kira suwaiba,ta shigo ta xauna
sai ahj qarami ya soma jawabi da cewa. tsohuwa
ina san ki xama sheda, yaran nan na ba yaya da
suwaiba har abada.ahj babba yasake rungume
yaran a jikinshi wani saban son shi ya ratsa shi.
idanshi suka kawo qwalla, suwaiba ta sa kuka
tace mun gode da wanna abu da ka yi mana.
Allah ya bamu ikon riqeshi da amana. ahj babba
yace bani da bakin da xan maka godiya, saidai
ince allah ya qara xumunci. ahj qarami yace haba
yaya dana nakane, saidai inasan abba ya xama
xaka kai daya. tsohuwa tace allah ya maku
albarka daku da yayanku, kaima allah ya baka
haihuwa. sukace amin. Sahura kuwa mijinta na
fita da yaro, itama ta xari hijabi ta nufi gidan
iyayanta, ta shaida ma mamanta cewan aminu
yayi kyauta da danta, kuma yaba mutanan da
basa qaunan ta. nan da nan uwar tahau masifar
cewan ba xai yuyu ba, ai dole ya baki danki.
shiko uban cewa yayi ai ikon sane, dan haka
baiga laifinsa ba dan yaba dan uwansa dansa.
sannan yace ,ta tashi ta koma. uwar tace ba xata
koma ba, ya ce ta xauna. bai sake bi ta kansu ba,
ya ci gaba da harkokinsa. shiko ahj qarami cewa
yayi baxai bita ba, lokacin da ya dawo ya samu
batanan, sannan bai fadama dan uwansa ba har
aka kwana. sukuma su suwaiba basu fahinci
sahura batanan ba dan ba hurda suke ba, saida
kukaxo cin abinki ahj qarami bai futo da kwanu
ba. sannan wan yace iyalin naka bata nanne?
yace yaji tayi, niko baxan bita ba. ahj babba yace
akan wani dalili ne? ahj qarami yace ban sani ba,
na dawo gida ban ganta ba. da safe ahj babba ya
tashi gaba sukaje gidan, sahura ba kunya tace
danta takesan ya dawo mata dashi, inhar yana
san xama da ita. Ahj babba yace, indai danta ne
xai maido shi. ahj qarami yace shi kuma inhar sai
an dawo da dan to ya haqura da auranta. kuma
na cikin ta ma inta haife shi xaixo ya ansa ya
qarama wansa inya so yaga yadda xatayi. duk
juyin da akayi yaqi yarda daga qarshe ma tafiyan
shi yayi. ubanta yace da ahj babba kaima jeka
yadda suka so haka xasu yi. satinta guda taka
abincin kirki gagaranta yake yi, ita kuma uwan ta
daina samun wani abu daga gun sahurar ke kawo
mata. dan haka suka yanke shawaran ta koma,
duk da haka saida ya shareta na kwana uku
sannan ya sakar mata. haka ta haqura saidai
tasha alwashin dun runtsi sai danta ya dawo
hannunta. sannan ta kulla sabuwan gaba da ahj
babba da suwaiba kuma tace duk tsohuwa ce
takitsa abin. abba yana samun kulawa tare da
tarbiya mai kyau.sahura ta haihu ta sake samun
da namiji aka samasa bashir, daga nan haihuwa
akai akai.. Tun abba yana qarami ya koyi wasu
halaiya na ahj babba. da farko, sallar
asuba,axahar, laasar, magrib da isha. ahj babba
kan tasa abba suje masallaci da rana kuma
umman sane ke turashi. ranan jumaa ahj na
dawowa gida dan ya tafi dashi. dan haka sallah
ta xauna ma abba da xaran lkc yayi xai fara shiri
yi. sannan ya iya sadaka dan dasunje yana bashi
kudi ya rabama almajirai ko yasa a asusun
masallaci. sai xumunci aduk lkcn da ahj babba
xashi xanfara yana tafiya da shi. ya tashi da san
iyayan shi matuqa bai taba sanin basu suka haife
shi ba. duk da cewan duk lkc da ya shiga gidansu
umman bashi takan cemai bafa umman kace ta
haifeka ba, nice na haifeka. riqonka muka basu. in
yaji haka sai yace allah kiyaye. sai ya baro gidan
ita kuma taita xakinsa. inya fadama umman shi
saitai murmushi ta rungume shi. ya ce aidai kece
ummata ko? ita kuma tace nice ummanka rabuda
ita kaji. abba yanada tausayi dan haka ya
taimaka ma ummanshi aikin gida. shekara sha
biyu ya sauke kur'ani.a lkcn ne ya gama pry ya
samu xuwa js1 Abba makarantan masu kudi ya
ke yi.ita kuma sahura duk yaranta ta batasu,
musamman bashir. duk lkcn da akace yaje
makaranta inyace ya gaji, saitace ya xauna kaje
gobe. ko ahj babba ya korashi sai dai ya labe
inya tafi shi kuma ya dawo. yafi san xuwa qwallo
ko shagon game. to hakama qannansa duk sun
dau irin tarbiyyan uwarsu. cikin haka wata ran
umman abba ta tashi da matsananciyan mura,
lkcn ahj babba yaje legos don taho da kaya. ahj
qarami ne yakaita asibiti bayan gwaje gwaje, an
gano ciki wata biyu da yan kwanaki. murna gun
ahj qarami tamkar yayi tsuntsuwa yaaje ikko ya
fadama ahj babba. suna isowa ya shiga gun
tsohuwa ya sanar da ita. nan take tasa kukan
murna.ita kuwa suwaiba tamkar mafarki, sai
kunya ta isheta. lkcn da ahj qarami ya fadama
sahura, sai cewa tayi um, bana an tabuka, ni dai
gani da cikin na shida amma sai yauxu ta samu
daya. ahj qarami yace kinji matsalanki, ke ba dai
kiji wani ya samu qaruwa ki taya shi murna ba,
sai dai baqin ciki. ta ja tsaki bakin cikin me
xanyi? tunda ni ga nawan. ciki mai laulayi
suwaiba ta samu, wanda duk abin da taci sai ya
dawo. wannan lamari ya daga ma ahj babba
hankali da abba, duk aikin gidan abba ke yi, ga
makaranta, ko an hanashi sai yayi.dan haka aka
dauko harira qanwar suwaiba, wanda mijinta ya
mutu. umman abba dai bata samu kanta ba saida
cikin yayi wata biyar. sannan ta samu sauki.lkcn
sahura tanada cikin wata bakwai, lkcn haihuwa ta
haifa mace, murna gurinta kamarme, dan sai
yanxu ta samu mace. safiyar talata umma ta
tashi da naquda, hankalin ahj da abba ya tashi
matuqa. duk da tsohuwa tana ta kwantar masu
da hankali, ranan abba ko makaranta bai jeba,
duk da san makarantansa, har suka dawo sallan
axahar shuru. ahj babba yace tsohuwa bari na
samo mota akaita asibiti. tace to. yana fita ba
jimawa ta haihu. ta santalo yarta mace mai
matuqan kama da ahj babba. tsohuwa tace da
abba,mai sunan mlm bi su ahj kace sudawo ta
haihu. dama harira tasa ruwan wanka lkcn da
suka xo ta fito daga wanka.nan aka wanke
yarinya yan barka sai xuwa suke amma sahura
saida aka. Sahura saida aka kwana sannan ta
shigo. ta dauki yar ta taba baki tace wannan yar
baqinqirin haka sai idanu daqwa daqwa. wata
mata da taxo barka tace ai wannan yar sak
abba,suna kama sosai. sahura ko kunya ta ce
basa wani kama da abba. da tasamu kyan abba
da tayi kyau, umma tayi ma matan alama da
haunu tai shuru. ranan suna taci sunan tsohuwa,
wato habiba, dan haka umma ke ce mata ummi.
abba yana ji da ita, saidai in yanasan tsoka nanta
sai yace dubeta ta ba ummata wahala, sai na
xaneki kika girma kika qi mata aiki. umma taita
masu dariya. tsohuwa ma naji da ita dan guta
take wuni. tunda ga kan ummi umma bata qara
haihuwa ba. abba yana aji uku suna qoqarin xana
(j.s.c.e)ya dage sai ahj ya saka shi shagon dinki.
ahj yace abba kabar batun dinkinnan ka tsaya a
karatunka. yace ahj nidai ina so kaga inna iya su
umma sun huta dakai dinkin su gidan laminde.
umma tace ka barshi yayi ahj sana an hannu ai
tanada dadi, kaga in ya gama bokon ba bai samu
aiki ba xaya riqe kanshi da sana anshi. ahj yace
to shi ke nan Ahj yace, to shi kenan, wane shago
ka ke san shiga inkai ka? yace, na can bakin titin
nan, in da kake saya na lemo. ahj yace shi kenan.
mafarin shigar abba gurin koyan sanaa kenan.
ummi ta taso da rigima, tsiwa tare da tsokana,
wanda yasa suka daina shiri da abba sam. abba
ne ya kaita makarantan boka da islamiya, kullum
yaje daukota sai ya raba fada ko ya bada hakuri.
umma kullum addua take fili da xuciya da lokutan
sallah, allah ya shirya mata ummi. ita kuma tata
kalan quruci yan kenan inta girma xata daina.
tsohuwa takance aini me sunana kingama min
komai, domin banasan ragon da, da in kai qara
gara akawo min na bada haquri. duk lkcn da tayi
wannan kalman sai sunyi fada da abba, dan cewa
yake ai dama tsohuwan nan tuni na ane kin daure
mata gindin ta siqa tsokanan yayan mutane. ita
fa mace ce ba namiji ba, shi kenan bata da aiki
sai dambe? tsohuwa takance batta tayi. tunda
ganan abba basa shiri da tsohuwa. ita kuma fati
yar sahura kamar ummace ta haifeta dan bata da
hayani. ummi kuma kamar sahura ta haife ta.
Wata rana abba ya ke cewa, umma da ace lkc
daya kuka haihu da umman bashir, allah cewa
xanyi kunyi canjin yaya. umma ta dube shi dan
me kace haka? yace sbd masifar ummi irinna
umman bashir ne, fati kuma ba ruwanta kamar
ke.dariya kawai take yi. kwanci tashi ummi ta
gama pry, lkcn abba yana shekaranshi ta qarshe
a jamia. yana karantan (mass comm)ne dan yana
san xama dan jarida. umma tasoshi da likita
amma yace baida raayi. tace kaga kai bakada
hayaniya abba aikin jarida na masu maganane.
yayi murmushi yace umma kenan. ummi ta samu
shiga aji daya a qaramar sakandare. maimakon
hankali abin nata sai gaba yakeyi. aduk lkcn da
tai laifi abba ya daketa sai tayi wani abun dan
tabashi haushi, da sunan ta rama. ahj babba ya
bude mai shago, tare da xuba mishi kekuna.
tsohuwa tace dakai wanine mai sunan mlm, saika
tafi da takwarana ta koya. abba yace ko a
kwafan shago na na ganta ba sai na karya mata
qafa ba. ummi ta murguda baki, sai daya tafi
sannan tace allah ya kiyaye inje wannan qaxamin
shagon nashi. Tsohuwa ta ce,"tafi can kema da
baki son ci gaba, in banda abinki da zaki kwantar
dakai ki koya in an tashi auranki basai a saya
miki keken ba. in kuma shi kika aura kinga
shikenan inya samo dinkin da yawa saiki taya
shi, ta ce"Allah ya kiyaye me xanyi da yaya
Abba,yayi ta cin xalina?ni bana son shi" Umma
dake gefe tana jinsu ta ce,"ke in kin samu kamar
Abban ma ai kinji dadi,shine zai ce mai zaiyi
dake? mara hali irinki." Ummi dai tayi shiru tasan
inta cika surutu kan Abba yanxun nan umma ta
doddoketa,umma tafi son Abba fiye da ita. watan
ramadan ya tsaya,duk daukacin musulmi sun
dauki azumi ranar da akai na uku Abba ya shigo
gida karfe daya saura. daga shago yake zaiyi
wanka yaje makaranta don yanada darasi karfen
biyun rana. Gidan shiru kowa na bacci,don haka
bai shiga dakin umman shi ba don baya son ya
tasheta ya shige bandaki. Da ya gama ya fito ya
nufi daki kamar ance ya kalli madafi, ummi ce
tsugunne tana cin abinci. ya tsaya yana kallonta,
dagowan da xatayi suka hada ido, yace ke! karya
axumin kika yi? ta toshe bakinta sannan nace
dan allah yaya kayi haquri. yace fito muje. ya
kaita dakinshi yasata gwale gwale. da xashi
masallaci ya kulleta ta baya. ya ce inyaso ki
tashi kafin na dawo, xan gane. yana fita tahau
binci ken abinda xata lalata mashi. ta ciro bidiyon
da yake kallo xata doka da qasa, sai taga kwalin
wani kaset tana kallon hoton jikin kwali, na
tsiraici ne. ta xare ido kicin mamaki, tace lalle
yaya abba, daman shi dan iskane? to kuwa xan
tona mai asiri. ta turashi cikin xaninta, da taji
motsin shi yana bude qofa sai ta koma inda take.
ya shigo ya kalle ta ya ce nasan kin xauna dan
kinga bananan. ya xauna bakin katifa, sannan ya
dubeta fuska daure. ummi meyasa kika karya
axumi? tace ba komai. yace tunda aka fara axumi
kike karyawa ko? tace yaune kawai yaya abba.
yace kinsan hukuncin wanda ya kasya axumi da
gangan. Tace eh an fada mana a islamiya, amma
mlm yace sai wadanda axumi ya wajaba akan su.
ya kalle ta cike da mama ki, a xuciyanshi yana
cewa, yanxu har yarinyan nan tasan akwai
wadanda axumi ya wajaba akansu? afili kuma
yace lalle ummi kina buqatan sa ido. dama
saboda bai wajaba akanki ba shiyasa kika karya?
to daga yau xansa maki ido, kuma xan fadama
umma ta sa maki ido. hakanan duk wani abu da
akeyi lkcn axumi an daina qyale ki, xaki ringa
sallar tarawi, ke har tahajjud sai kinyi shi. sannan
bayan axumi saikin rama wannan axumin. ya
xuba mata ranqwashi a tsakiyan kanta ,tare da
cewa tashi ki fita munafuka. daga dakinshi bayi
ta shige ta qara kallon kwalin, sannan ta maida
ta soke shi, tace sai na tona maka asiri. da dare
bayan angama bude baki, abba xai tafi tarawi ya
shigo dakin umma yace ina ummi? umma tace
gatanan kan kujera tayi sharkaf, wai yau taji
axumi. abba ya shiga ciki yana kallanta. yace
umma xaki yaudara ko yar rainin wayau, tafa
karya axumi daxu da rana na ganta tana cin
shinkafa. Yace shine kika xube wai ke kin sha
wuyan axumi ko? umma ta dube ta tana mamaki,
tace abincin da kike kinba almajirai da ma qarya
ne? ya dubeta yace biyu kenan ga larya axumi ga
qarya, xaki sani. tashi muje salla ko in ballaki.
umma tace allah ya shiryi halinki. abba yayi
dariya tare da cewa, kema dai umma yaxaki
amince da batun wai tac almajirai abinci, su basa
axumi ne, umma tace tunanin haka sam bai xo
min ba. saida ya sakata sahun salla, sannan ya
nufi gun maxa. bayan ya gargadeta da cewa in an
idar ta jira shi, inyaxo batanan sai ta sani. koda
aka idar da yaxo bata nan gurin ya kaure da
dambe da wata yarinya wai da suna sallah tana
bigeta. shine daga idarwa ta cakume yarinyan da
fada. bai tsaya sauraranta ba ya cire ta kalmi ya
shiga dukanta, sannan ya tasata xuwa gida. sai
da ta shige dakin tsohuwa sanna ya koma nashi
dakin. hakanan suka ta xuwa masallaci har
axumi yakai ashirin. Ahj ya kawo masu shadda
da leshi da atamfa na sallah ita da umman su
bashir da fati. ya suya masu takalma da mayafai,
abbane xai masu dinki, ran ummi baya son dinkin
abba, domin wanda take so bashi yake mata ba.
ta ce umma dan allah nidai a bani dinkina na
kaima laminde, yaya abba baya min ne kyau.
umma tace kije ki karbo da kanki. tace ai baxai
bani ba ne, xai dakeni. umma tace ai nafi san ya
dake kin, lamindan finshi dinki mai kyau tayi ne?
ummi tace nidai gara ita. tsohuwa tace ai banga
lkcn da mai sunan mlm xai faranta ma takwara
ba, kullun burinshi ya quntata mata. umma tace
tsohuwa ummi fa ba a mata gwaninta, inace dinki
in yayi mata har aro ake xuwa yi? ta dube ta
tace keda shine inya jiki kyayi biyu babu, yaqi
maki dinkin luma ya hana kayan bare kiba
laminde inga ta tsiya. qarfe dayan dare ya tura
dakin tsohuwa tana xaune a kan sallaya tana
addua, abba yayi murmushi. tsohuwannan kina
birgeni dama kina ibadan dare? ya kalla kan
gadonta, ummi taya dai dai tana ta bacci.
ZURFIN CIKI
Part 3
Marubuci : Abdul Nassir @AbdulNetwork
Ya kalla kan gadonta, ummi taya dai dai tana ta bacci. Yace, ummi ke! ummi!! tashi. tsohuwa tana yi masa alama da hannu gami da gyaran murya, wai ya bar ummi maimakon haka ma sai ya dauki wani kofi nan gefansa da guntun ruwa a ciki ya watsa mata a fuska. ta farka firgigit, yace taso, da sauri ta tashi yace dauko hija binki maxa. ta dauka suna fita tsohuwa tana sallamewa. tace kai mai sunan mlm ka lafama yarinyan nan haka, wai axumi wajaba akanta yayi da xaka tasheta da tsohon darannan xuwa masallaci? yace kema in xaki, xo muje. ya tasata suna tafiya tana hada hanya suka tafi tahajjud. sai qarfe hudu na asuba aka tashi. ummi har kuka tayi saboda tsananinjin bacci, amma tana tsoran kar ta kama bacci yaxo ya same ta. tun tana layin bacci har ta gyagije. sakamakon tashinta da matan kusa da ita keyi. kafin kwana uku ta saba da sallan dare, lkc nayi xata farka. abba yana xaune ga dinki gabanshi amma yana can tunanin bushira, yarinyan da yake matuqan so ce. amma yana shakkan fada mata,dan iyayanta sunada kudu matuqa. kuma shine yakema duk yan gidansu dinki. Ahmad abokinshi da ke gefe kuma sai yayi murmushi, yasan tunanin bushiqa ne ke damun sa, dan haka sai ya ce, abba kasan allah, abari ya huce shi ke kawo raban wani. haka kuma ZURFIN KICI, ba xai kai ka gaci ba. ka fada mata kawai. abba ya ce hum ,ina tsoron kada ta ce bata sona, dan bansan ina xansa raina ba. ahmad yace daga ganin yadda take jin kunyanka tana sanka. abba ya kalli ledan da ke dauke da dunkunan su bushiran, yace ina xatan yau xasuxo amsan kayansu, dan tun jiya nace suxo.ahmad yace to in sunxo kayi qoqari ka fada mata mana, indai ba ragon namiji kake ba. abba ya tsurama qasa ido yana tunanin in sunxo mai ce mata? kusan awa biyu sukaje sukai sallan axahar, tungan motan ta tsaya yasan tasu bushurane. shi kadaine a shagon sauran basu dawo ba. bushura ta shigo da qannansu da yarsu aisha. ya taresu da faraa, suka gaisa kan bushura na qasa, sam bata iya kallan abba tela kamar yadda suke kiranshi. Ya tura masu kayansu suka duba sunata murna dan ya masu wadda sukeso. aisha ta aje masa cikon kudinsa kan table. har sun fita yagadai baxai iya hakuri ba, yace bushura xo gashi. ta juyo tana dariya taxo. yace bushura inasan na fada maki wata magana gashi kuna sauri ko? ta kalli motan tace fada min. yace kina sona? ta xare ido sannan ta ruga da gudu. gabanshi na faduwa, bata tsaya ba sai mota. ya kwantan da kanshi akan keken yace menene maanan gudun da yarinyannan tayi? ya tambayi kansa, qarfe uku sunada lecture, amma baya xatan xashi makarantan. ahmad ya dubi abba wanda daga ka dube shi xakasan yana kin damuwa. yace wai banaga sunxo ba? ko ba motan su bane? shiya bandawo ba nakuma hana yaran dawowa dan ku sasanta. abba yace um, inaga yarinyannan gara na haqura, dan bana san insa kaina cikin tunani. ahmad yace ban gane ba, abba yace, to naga daga tambaya tana sona, saita kwasa da gudu ta shige mota. ahmad yayi yar dariya sannan yace ,amsan ta baka. tana nufin tana sonka. abba ya harare shi kada ka maidani dan iska, ina ta magana ta xabga da gudune shine tana sona? yace jeka tambayi manya .yaci gaba da cewa kaine baka mata magana da hikimaba, ka fito mata kai tsaye baka sakaya ba. abba yace, kai nifa ka sanni ba ruwana da wata kwana kwana, idan abu yayi min bana kwana, inko bai min bama haka, ni ba ruwana. Ahmad yace sai xurfin kici ko? da ya aka shawo kanka ka fada mata,abba ya mike tare da kallan agogo, yace inada lecture. gida ya nufa dan shirin xuwa makaranta, har yayi kamar ya tambayi ummanshi cewa in ka ce ma mace kana sonta taji kunya ta gudu wai alamun so ne? sai kuma ya kasa, yana jin nauyi amma in bai samu wata manufa ba dole yaxo ya tanbaye ta dan baya boye mata komai.bushura yar ahj sale ce kwamishinan gona na wannan xamani, gidansu yana karkasara. danqareran gida ne ginin xamani, sun san abba ne sanadin dinki da yayi wa wata qawansu jamila.dinkin yayi matuqan birge su dan haka suka fara kawo masa dinki, tun ranan da ya fara ganin su bushura ta kwanta mashi a rai. to ashe ita ma yamata.shiyasa yau daya furta mata take ganin kamar anmata gafara da aljanna.wata xuciyar tace ,to yanxu da kika gudu in ya xaci baki sansane fa, nan take hankalinta ya tashi har tana rayawa ga abba can da wata.dan haka taga dolene ta koma gun sa inhar tana sansa. dan tasha ganin mata na masa tayin kansu in sunxo kawo dinki.nan ta soma tunanin wace dabara ce xatayi ta fita?saiko ta warware daya siket din kayanta cikin dare.da safe ta nunama momynsu tace mata telan ya manta bai hada wannanba,dama yace xai gwada nine kafin ya hada.momy tace direba ne xai kai mashi.bushura tace momx xaifa gwadani ne muje dai xa kaini.tace to kuje, bushura ta danyi gayunta suka tafi.saidai kash! bata samu abba ba ance mata yana gida. tace gidan da nisane, aka ce mata babu nisa,dan haka ta sa aka rakata.tacema direbansu tana xuwa telan na gida.gidan ba nisa. A qofar gidan su abba ta tsaya, sai ga ummi ta sheqo da gudu tana dawowa daga aike.ta tsaya tana kallan bushura, sannan tace lafiya?bushura ta dubeta. yauwa abba yana nan?budan bakin ummi sai tace yaje kashi ya fada a masai.bushura ta dafe qirji, yaushe? ummi tace oho.sai ga abba ya futo sanye cikin shadda bulu mai duhu yana ta qamshin turare.shawara ya yanke lkcn da yake xaune a shago kan cewa yaje gidan su bushura,tunda gidan kwamishina ba boyayye bane,suka hada ido da bushura,ta saki faraa sannan ta dubi ummi,kince ya fada ina? ummi tayi ciki da gudu.ya bita da kallo sannan ya kalla bishira,me tace maki?bishira tace, ba komai.saidai dariya da maganan ummin tabata.yace tunda baxaki fada min ba xomuje ki gaida ummana.cikin muryan jan hankali tace ina jin kunya.ta bude jakanta tace kamanta baka dinke wannan siket dinba.yace mugani,yaga yadda aka warware shi aka cire xaran da kyau. murmushi yayi dan yasan ya dinka siket din,kusan shinema na farkon dinki.ya gane yaran nata qila san ganinshi take san yi. Ya dinke siket din yana cewa"to amma sai dai ayi min izini inzo gida in kawo da kaina in na gama." tace haba dai,ya za ayi in taso ka?"ya ce,"ba komai,in dai anyi min izini sai inzo," ta ce,"to in maka kwatance?" ya ce,"a'a huta kada ki bata bakinki,nasan gidanku zanzo anjima bayan tarawih." ta ce,"to." sai mun zo" tace"ku dawa? ya ce,"abokina mana,kinga zo muje gurin ummana ku gaisa." Bishira ta bishi cikin jin kunya.tun kafin su shigo daman ummi ta shiga gurin umman da gudu tace mata"umma ga budurwar yaya Abba." Umma tace budurwa kuma? tace eh ai zama su shigo.daga nan ta kara kyallawa dakin tsohuwa tana fada mata. Umma dai jim tayi dan bata da wani burin da ya wuce ta baiwa Abba ummi,kuma da tasan har zai ga wata can da wuri haka data fada masa kudurinta,sa tay 'ZURFIN CIKI' gami da nauyin baki....... sallamar Abba ce ta katse ta ta ce,"shigo Abba." ya ce Umma bakuwa ce taxo gaisheki.Umma ta fadada fara'arta tace to shigo,ba dai surukar tawa bace?" ya ce,"ai ita ce kam" Bishira ta shigo tana sunne kai,ta gaida umma Umma ta ce,"masha Allah,Allah yasa rabon muce."Abba yana dariya ya ce,amin ummana."ya dubeta,"tashi ki gaida kakata." suka nufi dakin tsohuwa,umma ta jinjina kai .tabbas Abba nason yarinyar,in ta dubi yanda yake fara'a da zumudi. a fili ta ce,"Allah yayi mana zabin alkairi."ummi na kwance kanta na cinyar tsohuwa,sai ta kalli bishira ta tuntsure da dariya,lokacin da suke gaisawa da tsohuwa. Abba ya ce,"dariyar uban me kike yi?" sai ko ummi ta sake shekewa da dariya. ya nufota ya suri kafafunta,tsohuwa ta ce haba mai sunan malam yanxu in bata yi dariya ba kuka zatayi?" ya ce,Bishira tashi muje" Tsohuwa tace to yanmata mun gode ki gaida magabatan naki,sannan kiyi ta hakuri da halin wannan miskilin." Umma ta ce,"tsohuwa kodai kishi ne?suka yi sallama,ummi wadda tunda ya shureta ta rigasu fita sai ta dauki takalmi Bishiran guda daya takai soro (zaure). don haka da suka fito suka shiga nema ummi ta kule uwar dakin umma tana ta dariya tana lekensu. Abba ya ce,"ummi! ummi!!" taki amsawa ya nufi waje da niyar dubota don yasan ita ce zata dauki takalmin,sai ga takalmi a kofar shi. Don haka ya dauko kawai ya dawo ya bata umma ta ce,"ka kaita su gaisa da umman Bashir." Abba ya ce,"a'a ba yau ba."ya rakata wurin direbansu,kusa da shagonshi sukayi sallama da alkawarin zai zo washegari. yaje kuma bishira ta fada masa lallai tana sonsa sai dai tana tunanin iyayenta ko zasu amince? ya ce,to shi dai zai turo magabatansa su nemar masa izinin zuwa zance kamar yanda yake a shari'a Bishira tace a'a ya bari tunda yanxu shekarar farko take a babbar sakandare(s.s.1)ba za a bari ya dinga zuwa ba,amma zasu dinga haduwa gidan yarta dake na'ibawa. Abba baida zabin da ya wuce ya yarda da hakan tunda tace baza a barta yin tadin ba.sai dai fargabar shi kada nan gaba sunyi zurfi cikin soyayya ace ba za'a bashi ba. ta ce,"Babana bashi da matsala,amma momy dinmu ce abin tunani."Abba ya ce,"shikenan Allah ya shige mana gaba." soyayya ce mai karfi ta kullu tsakanin Abba da bishira,wanda har ummanshi da kanta tasan cewa Abba yana son yarinyar. Domin duk lokacin da zaije gurinta tana lura da zumudin da yakeyi,kazalikain tace ka gaida surukar tawa, bakinsa baya rufuwa. Don haka sai ta tattara batun ummi ta aje a gefe addu'a ce kadai bata daina ba.ana sauran kwana uku sallah.Abba ya siyo fenti yazo da mai fentin nana ak fente gidansu ciki da bai. Da yamma kuma ya kawo dinkunan su ummi da fati,ummi tasa ihu,sam irin dinkin da ta aro gurin kawarta Amina ba shi yayi mata ba,ya zai mata dink iri daya da fati? ya ce,"kin isa ki sani in miki dinkin da kike so?ta ce to ni dai bazan sa ba umma ta rafka salati tana kallon ummi ta ce,"ummi kina da hankali kuwa? kudi kika biya ko ko Abban sa'anki ne?" tace cikin kuka to ni umma ya zai min iri daya da fati? ya dubeta a fusace,"in kin bari na dauki kayannan wallahi bazaki sasu ba." Umma ta ce,"ni da zaka daukesu ma da naso"tsohuwa ta fito ta ce,"saboda me? akan wane dalili zaka amsar mata kaya?tunda baka mata wanda take so ba sai ka kyaleta." Da hannu Umma tayi mishi alamar yayi shiru,sannan ya fita waje.Abba ya kada kai ya fita. washe gari kuma ya shiga da me fenti har cikin gidan Alhaji karami,sahura tana daki lokacin da yake nuna ma mai fenti guraren da zaya fara. Ta fito daga daki ganin Abba sai ta hade rai sannan ta ce,"mune kashin baya? ai dama ka bar shi tunda baka mai da mu wani abu ba,mu ne dai baka so din mahaifanka. Ta dalilinmu zaka shiga aljanna,ba dalilin wasu banzaye ba da sauri ya nufi hanyar fita waje don baya son yaji zagin da zata yiwa Alhaji da Ummanshi. wannan na cikin dalilin dayasa baya son zuwa gidan Alhaji Babba da Umma,sune suka ci kashi da fitsarinsa. suka bashi tarbiya da ilmi,suka ci da shi suka shayar dashi.amma sam basa yi masa abinda umman Bashir ke masa. haihuwarsa ce kadai su Alhaji babba basu yi ba,sahura tana zuwa har shago tayi masa rashin mutunci,sannan ta ce ya bata kudi,ta ce ya ba bashir kudi ko ta aiko fati. Bai taba kin bata ba,amma duk da haka bai tsira daga zagin rashin mutunci ba.ta ce ya tare a gidan ummanshi komai nashike mata,wai da kuma sam ba haka bane. Umma bata taba tambayar shi sisi ba,haka nana duk lokacin da ya bata wani abu ko ya sai mata,sai tace ina na umman Bashir? kaje itama ka bata,in ko bashi da yawa ni naci girma ka bata. Ranar sallar idi kuwa ummi koda tayi wanka kin saka sabon kayanta tayi sai na bara. Lokacin da zasuje sallar idi,Abba ya fito daga wanka ya kalleta ina kayanki sabo? ta tura baki"ni baxan sa ba." Yace,"to zanga wanda zaki bi masallacin,kuma ki kara magana saina fasa bakinki."sai ta wuce kofar dakin tsohuwa,sannan ta ce,"to ai dai nima nasan hanya,kuma sai naje."ta fada dakin da gudu. ya bita bata san yaga tsohuwa lokacin da ta shiga wanka ba,bayan fitowarsa.don haka ya ritsa ta ya kwakkwada mata mari,sannan ya rike mata kunne. zan kara fada ki fada? ta ce,"a'a kayi hakuri." ya saketa ya wuce,ta zauna tana kuka. misalin karfe hudu na rana ,bishira ta iso shagon dinkin ita da direba,shagon a rufe.don haka ta ce su karasa gidan. Can dinma baya nan,amma sai ta fito ta shigj gidan dauke da tire babba cike da kuloli. cikin kunya ta gaida umma,ta kuma bada a aje masa.umma ta ce,"to ko ina Abba yayi? kila gidan su Ahmad yaje."umma ta ce,"ke uwar gudu ina yayanki?" ta ce,"nima na ganshi?" karar bude kofarshi suka ji,ta ce,"leka in shine kice yayi bakuwa.shine kuwa,jin cewa ga bishira ya shigo da zumudi. Umma tace ka kaita ta gaida umman bashir. yace to, ta fito ta tafi kicin ta bar masu dakin,ashe ummi tana uwar daki tana jinsu.ya ce,yanxun fa daga na'ibawa na ke,ina ta xumudi in ganki. tace,na xaci ba xa kaxo ba ne,nace bari inxo ni,dan baxan iya kai dare batare da idanuna sunganka ba.ummi ta toshe bakinta saboda dariyan da yakesan kufce mata,yace sai inga kamar bakya sona.bishira tace haba abba, in kace haka bakamin adalci ba.yace to wadannan kulolinfa me kika kawo min?ta ce bude ka gani.ya bude ya gani yace kai, lalle ashe ni dan gatankine? tace sosai ma.ya marairece murya yace to bani abincin a baki.ummi daga cikin dakin tace, la'ilaha illallahu.abba ya miqe da sauri.kafin ya ankara ummi tayi fitan bindiga tsakar gida tana fadin la'ilaha illallahu,dama yaya abba dan is....umma ta gwabe mata baki,bayan ta fito daga dakin ahj babba.ummi wadda inta s6a magana ko ana hanata sai ta kai aya.ta dafe baki,tace maci gaba da fadin,umma to kinji abinda yake ce mata ne? umma ta jefeta da takalmi tare da cewa,wai baxa kiyi min shuru ba? ummi tace,to fa cemata yayi xai bata abinci a baki,kuma daman xan nuna maki wani kaset da yake kallo. Abba ya riqe kai tare da cewa ummi in na kamaki xaki sani, kaset din wa kikaga ina kallo? tace na yan is....da gudu ya bita ,yayin da umma ta jefa mata murfin kwano,amma duk haka ko da ta fita waje saida tace masa sai na nuna ma ahj kwalin kaset din.take ya tuna da kwalin kaset din daya boye,wanda ya qwace a hannun bashir,kaset din tsiraici ne wanda laanannu sukayi.abba cikin takaici yace,kai ummi! kai ummi!! kinsan allah in kina wasa dani xa karyaki a banxa.ta ce to ba a dakinka na gani ba?yayi qwafa,allah ya sani ya tsani ummi kamar ya shaqeta ta mutu.sai ya samu kanshi da qin komawa gidan,kunya da nauyin umma yake ji,yasan dai ba xata kama xancan ummi ba,amma yasan xuciya da xargi,qila xuciyanta ta xargi wani abu.bashir ya fito daga cikin gidan su abba yace,yauwa bashir shiga gidanmu kace bishira taxo. Bashir rai bace ya shiga,dan yana jin haushi ya amsar me kaset.ya shiga umma na qofar kicin xugun tana tunanin halin ummi.bashir yayi sallama umma ta amsa.yace,abba ne yace in kira bira ne ni yace ne?umma tace gatanan ciki,taxo bakin qofa ta kalli bishira kanta na qasa tana mamakin ummi.yarinyan sam bata ji.umma tace kixo yana kira awaje.cikin kunya ta fita, yace da bashir rakata gun ummanka su gaisa.bashir yayi fara,a antynace ke nan?abba yayi murmushi. bishira ta xauna gaban ummansu bashir suka gaisa. bashir yace,budurwan abba ce. sahura tace,yau kika taba xuwa nan unguwan? kanta na qasa tace, xuwana biyu kenan.ta kalli bashir tace kaji ko? amma shine ko a turo ta nan gidan.nina haifi abba amma an gaje min shi.tace yarinya duba nan.bishira ta dubeta,ta dafe qirjinta ni na haifi abba nine uwansa.matan gidan can mai gidana ya bada shi a gunta,da ubansa da maigidan dan wa da qani ne amma sun gaje shi.bani da ikon sashi ko hanashi amma sun mallakemin shi. da muryan tausayi take maganar. Bashir yace, umma indai ya aurota xamu samu sauqi.bishira tace kada ki damu, insha allah komai xai warware. tace, to yan nan na gode.fati ta shigo ta gaidata cikin nutsuwa, bishira tace wannan qanwansa ce? umma tace eh, ai su ga sakamakon mugunta nan sun haifi yar muguwa mara jin magan. bishira tace, kai yarinyar bata ji. fati ta ce abba ya ce kixo.sahura tace kinji ko? shifa ko nan gidan baya qaunan shigo wa.bishira ta miqe ta balle jaka ta ciro sabbim kudi yan ashirin ko irgawa bata yiba ta bata, tace kinsaya goro.sahura tace harda abin arxiki?to an gode.bashir yace antyna inane gidanku?tace karkasana gidan kwamishinan gona.bashir ya raxo ido, nako san gidan,lalle antyna ina qara gaisuwa.bishiratayi dariya.abba na tsaye suka fito,yace mata to ki tafi xanxo amjima. tace baka kaini dakinka ba.ya girgixa kai, bai dace ba wannan ba mutunci bane,sam bai kamace yar mutunci suna xuwa dakin samari ba. bishira tace danme? yace sharia bata amince ba, damin duk lkcn da mutum biyu suka kebe,musamman mace da namuji. Abba yace na ukun su shedan ne. irin wannan yana haifar da xinace xinace a bayan qasa.tace hakane ta tafi.abba ya rakata har mota, bashir kuma tamkar maroqi, sai fadi yake allah ya tsare antina ki sauka lfy.bayan tafiyanta abba bai iya shiga gidan ba tunaninshi daya kada umma ta xargeshi.dan haka ya nufa gidansu ahmad.ya ba ahmad lbrn abinda ya faru.dariya ahmad yayi tayi.yace kai amma wannan ummin taku yar dirama ce. abba yace cikin takaici yanxu kai har kaga abin dariya?yaja tsaki yace allah na tsana ummi, namata muguwan tsana. dubi wannan yarfin da tai mani. ahmad yace xata bari, wata ranama ko ance tayi watace sam batayi ba.abba yace taf wannan yarinyan dawuya in xata taba yin hankali, duk wanda ya aureta ya auran ma kanshi fitina.ahmad sai dry yakeyi. da magariba ya shiga gidan,cikin saa ya samu ummi tana cin abinci.nan take ya kama hannun ta har saida tayi yar qara, yace muje ki dauko min kwalin kaset din da kika dauka, Umma tace, Abba na soma tunanin yarinyar nan tan da aljanu da gaske. abba yace hakama alhaji qarami yace, amma fa anje babu kowa akanta. ya saki ummi bayan ya ranqwasheta. sannan ya ce, in kika sake yarda ki kaga wani abu a dakina kika dauka sai na balla ki. washegari abba ya tasa ummi ya nufi gurin masu ruqiyya, amma da aka mata babu kowa a kanta kamar yadda ya xata. ya dawo ya sanar da umma,umma tace na gode allah.halinta ne ita kuma irinta kenan? yace irinta kenan umma,baxata canxaba saidai muyi ta mata addua, soyayyan abba da bishira ta bunqara,har dangin abba sun san da batun,sahura duk tabaxa ma dangi.sanadiyyan maganan da tayi ma bushiran na cewa an rabata da daxta. wata rana bishiran tace masa xata xo gaida ummanshi,yace to cikin xumudi sai tace, umman su bashir fa nake nufi, ba ance ita ce mamanka ba? abba ya ce inji wa? inji ummanka. abba yace sam, ummana ba xata fada miki ba sai dai ko ita umman bashir din. tabbas itace ta haifeni, amma ba itace ummana ba.tace dan me? nan take ya hada rai. Abba yace mata ba matsalanki bane, so ban so ki saka kanki ciki. nan take ta yarda da batun umman bashir.ta a mince qwarai umman da abba ke kira umman shine muguwa ce.kuma itace ta raba abba da umman shi.dan haka saita tsiri xuwa gun umman bashir, tare da yi mata kyauta.shiyasa suka saba sosai.duk xuwan da bishira xatayi sahura saita kukkushe umman abba, tare da yi mata sheri. dan kawai bishira ta tsaneta,kuma bata xuwa gunta koda taxo anguwan. abba bai taba sanin haka ba,ita kuma umma bata taba fadan mai ba, dan ummi ta taba fada mata cewan budurwan abba tana xuwa gun umman bashir kuma bata xuwa gunki. umma tace nida umman bashir duk daya ne intaxo gunta tamkan taxo guna ne. sai kuma habaicin da take jiyowa ta katanga sahura nayi.har ya kai umman abba na ganewa in bishira taxo, domin inxata tafi xakaji umman bashir tana cewa,to na gode yar albarka bakya gajiya da abin arxiki,ai ko baki kawo min komai ba yancina da kika fara qwato min kin biya ni. kuma ina tabba tan maki inkinga abba bai aureki ba baya raye.
ZURFIN CIKI
Part 4
Marubuci : Abdul Nassir @AbdulNetwork
Wannan furucin ke sa bishira na qara shige ma
sahura, duk wannan sha'anin da sukeyi abba bai
sani ba. wanci tashi abba ya samu digree,
sannan yaje kamp din shi a damaturu jihar
yobe.sati biyu yayi sannan ya dawo. cikin sati
biyun nan da baya nan ummi ta baxa iya
shegenta son ran ta, umma ta qosa abba ya
dawo saboda yanxune ta gane tsoran abba yake
sa ummi tayi mata aiki da aike.dan tasan in ya
sani baruwan shi da pushin tsohuwa,xai
nakadetane, amma ahj da umma duk abinda
ummi tayi daxaran xasu hukunta ta xata sa masu
kuka tace dan de aci mata xarafine.shi yasa suka
sakama ummi sunanta,sannan kuma suke
dukanta a gabanta,imba hakaba maisa basuyima
mai sunnan malan ba?dan dole suke qyaleta ,duk
da ummi ta soma tasawa amma sam bata yi
hankali ba. shekarun ummi sha uku tana js2
amma ko yaushe qara tirewa ummi keyi. addua
kurun sukasa agaba,kuma sunsan allah xai amsa
masu. Ranan da abba xai dawo ummi ta kama
yima umma aiki da aike, dan kar a fadama abba.
a ranan ne ummi taga wata alama da ta
tsoratata cikin fitsarinta. a rudenta da hauka ta
nufi gun umma tana cewa, umma na shiga uku
na, fitsarin jini nake yi. umma tace, wane irin
kuma fitsarin jini? ummi sai tsalle take tana fadin
ta bani ta lalace. umma tace ke xonan. ta jawo
ta xuwa cikin daki, tace ke yimin bayanin yadda
kika ga abin. ummi ta cire xani xata cire siket.
umma tace, ke dakata min bance ki nuna min ba,
yaya kalanshi yace? ko da tayima umma bayani
sai ta fahince girmane ya kama ta. dan haka sai
ta kamo ta ta xaunar kusa da ita, tayi mata
bayani game da abin data gani, sannan ta nuna
mata hadarukan da take ciki a halin yanxu. tace
ummi ki natsu kiyi hankali, kisani yanxu kinkai
wani matsayi wanda xakiyi taka tsantsa da
rayuwanki. hadari na farko shine wasan banxa da
maxa, kece mara hankali indai kin sama abokin
wasa ba ruwanki da maxane ko mata ke dai kiyi
wasa, Umma tace kisani yanxu xaki iya daukan
ciki, indai har kika bari wani namiji ya shiga
harkanki. ummi tayi xullo tace umma ciki irin na
bara'atun baito? umma tace, eh ummi tace
wanda har suka yar da yaran aka xo aka kama
su yan sanda? umma tace tabbas. ummi cikin
fargaba tace to ni umma baxan yi ba. ta soma
kuka, to a kaini asibiti a bani magani mana.
umma tace duk bayanin dana maki baki fahinta
ba? ai wannan kin dunga yinsa kenan har
qarshan rayuwanki, ko kuma in kinkai wani
mataki na tsufa. ummi tace, to shi kenan, yanxu
kuma inna yi wasa da maxa sai in xama irin na
bara'atu? umma tace qwarai kuwa. ummi tayi
tagumi tana tuna yadda suke tsokanan bara'atu
inta fito. suna cewa tayi cikin shege tayi cikin
shege! ta dubi umma tace xan daina ma yan
maxa magana. umma tace ki dinga maganarki da
kowa, kidai kula da kanki, sannan duk sokanan da
kikayi da xunubin da ki ka kwasa to fa ki sani an
bude maki fayel. Umma tace xunubinki xaki
samu,gashi bakya san sallar kan lkc, sannan ga
karya axumi.ummi ta sake tsurewa ,tare da fadin,
to ba tsohuwa tace min inna mutu baxa ayi min
hisabi ba,wai ni yarinya ce wai makarantan
annabi ibrahim xa a kaini.umma tace da kenan
kafin ki soma kalar wannan fitsarin, yanxun kam
in kin mutn xa a tambaye ki a cikin kabari,
tambayoyi uku masu sauqi, masu wuya agun
mara rabo.sannan xa a maki hisabi inkinyi mai
kyau kiga mai kyau. tayi tagumi, umma ta manna
mata tsumma a jikin pant. tace tashi kisa in
kuma kinje gun haukan guje guje ya fado mutane
sun gani shi kenan asirin ki ya tonu, kowa yasan
kin girma. ummi dai ranan lafewa tayi kan kujera
tanata tunani. tana kwance lkcn da ake hayaniyan
dawowan abba kannanshi ne suka shigo mai da
kayansa. qasa ya xauna a dakin umma, ya miqe
qafa domin duk a gajiye yake. umma tayi ta dire
mai abubuwan ci wanda tasan yanaso a gaban
shi. sannan ta ba fati kudi ta sayo mai lemun
kwalba, dariya yayi ya ce,ni dan gatane, shiyasa
ina can ina tunaninki ummana, har nace inama
ana tafiya da uwa da na tafi da ke.umma cikin jin
dadi tace allah sarki abba, niko ina nan ina maka
addua allaih ya baka abin da kaje nema,yace
ummana kenan. ummi dai tana jinsu sam baima
gantaba, sai can ya lura yace a,a kekuma lfy?
umma tace bata dan jin dadine. yace tabdi,lallai
kuwa ciwan nan yayi tsanani, ummi da ko a
gadan asibiti take bata daina halinta? umma tace
ai yanxuma nasan lafawa yayi ko ummi na?
ummi dai kallansu take yi. abba yace allah ya
yaye. suka ci gaba da firan su yana bata lbrn
camp tare da nuna mata hotunan da suka dauka.
yace dan ba kusa bane da kunje min kunyi kallo.
ummi da xata bayi sai tafiya take wani iri tare da
ware qafa. saboda rashin sabo. tsohuwa tace a,a
takwara lfy? ummi tace, fitsarin jinin nake yi.
umma ta fito da sauri tace ke ummi xo. tsohuwa
ta saka salati, tare da cewa yarinnan nan badai
faduwa kikayi ba. ummi tace nifa ban fadi ba
hakanan ya xo min. umma tayi mata daquwa
tace bayin kenan? tsohuwa tace ke suwaiba
yarinyan nan faduwa tayi? da yake umma ta
fahinci hausanta sai tace um,lkcn tane yaxo.
tsohuwa ta saka salati tace, ni habiba yau naga
abinda ya isheni? yarinyan yar shekaru nawane
kwata kwata. lalle xamani, to sai ayi axaman
aurad da ita. umma tace waxai kula ummi da
sunan aure ni suwaiba? ki kalla haukan data keyi
a gari. abba cikin daki yace umma wa tsohuwa
take cema ayima aure? umma tace ummi itama
cikin dariya. yace tabdi jam to wannan takwaran
taki waxai kwasa, ga muni ga rashin hankali.daga
bayi ummi tanata murguda mai baki tana cewa
eh din. Tsohuwa kuwa masifa ta hau yi,"gaka nan
mara mutunci a gabana kake zagin takwara?kai
mai sunan malam ka kiyaye ni" shi dai ya fita ya
nufi dakinsa don kintsawa,yana mamakin ummi
ta zama babba. Koda umma bata fada mishi ba
ya gane haka ne ta yadda tsohuwa tayi maganar.
tsohuwa ta dubi umma ta ce,"ki na daure ma mai
sunan malam gindi yana ci ma takwara kashi a
hannu,alhalin yana zaune a inuwarta.nan fa gidan
ubanta ne." umma ta bata rai matuka,ta ce
"tsohuwa ni da Abba da ummi duk daya suke a
gurina,don Allah kada ki kuma furta haka har
Abba yaji. kai ni da za a ce in zaba tsakanin
ummi da Abba,na rantse Abba zan dauka."bata
jira abinda tsohuwa zata ce ba,tayi ciki abinta.
tsohuwa ta gama yan mitocinta ta shiga daki.
Kwana biu kamar gaske,ummi an nutsu, amma
abinda ya takura mata na daukewa sai umminku
ta ci gaba da gashi, sai ma abinda ya karu. Abba
ya daga ido sama yana kallon wasu tsuntsaye
suna ta shawagi a sama, zuciyar shi tana cikin
matukar damuwa sakamakon sheshshekan kukan
da bishira keyi, bata san cewa ya fita damuwa da
tafiyarshi kaduna ba? in ma da don ta ita ne da
sauki tunda gidansu da waya zai iya zuwa
(telephone) na bakin titi ya kirata. damuwar shi
umman shi. ta katse shi "yanxu Abba haka zan
daina ganinka?" ya sake tausasa murya."haba
bishira, ina kano ina garin kaduna?" ta ce, "tabdi,
nifa dalilin kukana taron matan kaduna nake ji, an
ce kwarjini garesu. kawai kaje ka sa samu wata
ka manta da batuna." Yayi murmushi "bishira
kenan, kada ki dauka son da nake miki mai rauni
ne da har zan canza wata dake, ni dai ki min
addu'a." ta ce,"sam ban yarda da wannan zancen
ba, ni dai bari in kira antina mijinta zai iya
taimaka maka a barka kano." kafin ya ce komai
tayi ciki da gudu. yayi yar dariya. bishira tunda
ya ce kaduna aka tura shi duk ta damu. Anti ta
fito daga kicin, bishira ta ce, anti kizo inji Abba.
anti ta dubeta, "in zo?" bishira ta kama hannunta
"don Allah aunty taimako zaki mana, zo ki ji." 49-
suka xauna sannan abba ya gaidaa anti cikin
girmamawa.bishira ta dube shi ka fada
mata.abba yace me?tace anti kinga fa kaduna
aka tura shi,ni kuma wlh ba xan so yaje garin nan
ba.anty ta sa dariya.to yanxu so kike yaqi xuwa
ko so kike ya tafi dake? tace,ni so nake ki yima
abban nasir bayani,nasan ba xai rasa sanin wani
da ya sani ba.abba da anty suka sa dariya,yace
kamar yaya?tace yayi magana a barshi anan
suka sake tuntsira dariya.tayi fushi ta miqe fuuu
ta nufi cikin falon gidan.anty tace bishira tana
matuqan sanka,dan allah ka kula da ita.ya kalleta
ya sunkuyad dakai,yace nima anti ina santa,kuma
tuni nasa manya susan xancan,saboda in samu
natsuwa,amma tace tana jin tsoron
mamanta.anty tace eh to,dole taji tsoro dan ba
dole bane hjynmu ta yarda,amma shi babanmu
bashi da matsala.abba yace to ni dai xan tura a
kowane lkc,dan ahjna yayi min magana tun kafin
tafi ta camp. Din nan yake ta min zancan." Aunty
ta ce,"to in kun tashi fa ba gurinshi za'a tura
ba,gurin kaninshi ne dake jakara.amma kafin
hakan sai an nemi izinin Alhajinmu din." Abba ya
ce,"to ni ko wa zai shige min gaba gurin neman
izinin?"aunty ta ce,"Abban nasir zan sanar
dashi,insha Allahu har wannan din ma batun
(service)din naka zan mishi bayani." cikin murna
abba ya ce,"to na gode,Allah ya saka da
alkairi"anty ta ce,"ba komai" ta mike "bari in turo
ta don nasan tana can tana cika sai ka bata
baki." yayi yar dariya tare da cewa"to". ta zauna
tana kumbure-kumbureya ce"haba tawan har
yanxu baki huce ba?" ta sake kauda kai gefe,ya
ce"to shi kenan,yanzun dai na fasa barin
kaduna." ta dube shi da sauri,"ka fasa barin
kaduna fa ka ce?" yayi yar dariya"au na
manta.kece duk kin ruda ni,cewa zanyi na fasa
barin kano." ta share yar kwallarta,"to shikenan"
ya ce,"naji dadin kiran anty da ki ka yi.ina ganin
nan da yan kwanaki su Alhajinku zasu sanni,Allah
yasa ace an bani ke." Wayyo dadi,ta tuntsure da
dariya.abbana nawa,bana zaton cewa zaka kai ni
murna a ranar."ya mike zan tafi "ta ce tun
yanzun? to ka ce ina gaishe dasu umma." Ya
ce,"umma bata cin mike,kullum sai ta ci in gaishe
ki da kyau.amma ke kin ki zuwa gaida ta." ta
ce,"kasan fa ni bana iya sakewa da ita,nafi
sakewa gurin umman bashir." ya ce,"kunyarta ki
ke ji?" ta dan tabe baki tare da daga kafada kila.
ya ce,"ina mamakin yanda kika saba da umman
bashir,alhalin ummana tafi saukin kai." ta ce,"ga
wannan kanwar taka mara kunya." ya yi yar
dariya sabida tuno abind ummi ta musu. ya ce a
hankali,"zaki saba da halin ummi."ta dube
shi,"tun ranar dana soma ganin ummi din nan fa
ban taba jin cewa ina sonta ba." ranshi yadan
sosu,har ma ya gimtse fuska,amma baice kala
ba.lura tayi da canzawarsa.don haka sai ta ce"ka
min afuwa in na bata maka." nan ma bai amsata
ba.illa sai da safe. Tamkar Alhaji yasan yadda
abba suka yi da antin bishira,da safe Abba yaje
gaida shi ya ce,"babana zuwa yanzun ya kamata
a ce mun shiga maganarku da yarinyar nan."
Abba ya sunkuyar da kai tare da ce wa,"um,dama
gidan antinta da naje dazu munyi zancen,yanzun
dai su ce sai an nemi izinin shi baban nasu. ta
ce,mijinta zai masa magana,in yaso sai kuji ranar
da zaku je din." Alhaji ya ce,"to shikenan.Allah ya
kai mu.yanzu yaushe zaka tafi kaduna?" kafin
abba ya bashi amsa,ya ci gaba da cewa,ban so
ba sam da wannan yin nisan da zaka yi damu
Abba." Abba ya ce,"ina hasashen cewa za a barni
nan kano da yardar Allah,bisa ga taimakon mijin
yayar yarinyar da nake zuwa gurinta." Alhaji ya
ce,"to Allah ya yarda,sannan in an fada maka
lokacin da zamu gana da waliyyan nata sai ka
sanar dani." Abba ya ce,"to." Alhaji ya ce,"ina son
mu danyi bincike kan yarinyar amma mahaifinta
sannanne ne,anata yabonshi." Abba ya ce,"to."
Ranar juma'a da misalin karfe biyu da rabi Alhaji
ibrahim (wato abban nasir,mijin anty farida),ya
samu sirikinsa a gida. bayan sun gaisa ya
tambayi yan jikokinshi sai Alhaji ibrahim ya
ce,"suna lafiya.dama makasudin zuwan shi
ne,akwai wani yaro da ke zuwa gurin
bishira,yawancinan gidanmu suke zance. to
gaskiya na yaba da hankalin yaron,sannan ya
damu yana son ya turo iyayensa.to shi ne nace
bari in nemar musu izini tukun." mahaifin bishira
ya kalli surukinsa ya ce,"aisha ko bishira?" Abban
nasir ya ce,bishira ce." ya gyara zama. "bishira
ta gama sakandare ne?" Abban nasir ya ce,"ai
Alhaji ba yana nufin ayi auren yanzun bane,a san
dashi ne." Alhaji ya ce,"bana haka,ka sani sai dai
tayi abu daya,in karatun karatun,in auren to
auran. Ibrahim kasan wani abu daya? duk lokacin
da kasa yarinya ta soma tsayawa da saurayi
bayan tana karatu,musammanirin bishira irin
wadda tasan tsarina amma ta danne ta turo min
saurayi to gara ayi mata auren. Domin doguwan
soyaryannan bata da ma'ana,qarshe sai wata
shedana ta biyo baya,balantana bishira tana da
rawan kai.ya matsa kusa da wayan tangaraho
wadda aka jona ta ke amfani a daukacin gidan,ya
dannan nanbobin sannan ya kira hjy.ta amsa
daga sashanta,yace bishira na ciki? tace tananan,
yace ki turo mani ita,tace to.gaban bishira ya
badi,ganin mijin yarta a gidan dan tasan abinda
ya kawo shi.ta xauna can gefe tace,gani dady,ta
gaisa da abban nasir.mahaifinta yace nasan
kinsan dalilin xuwan ibrahim ko? kanta a qasa
tace,a'a. yace.yace to saurayin da ce xuwa gunki
ne yake san ya turo magabatansa,kuma nasan
kinsan da batun?sai dai inasan kisan abu daya
bana san doguwan soyayya,da xara nagama
buncike akan yaran wanda shari'a tace.inna
gamsu,to fa aurad dake xanyi kije can ki qarasa
karatun in kina so.ahj ibrahin yace yaran yace shi
ba dole sai anyi yanxu ba.nufin shi a amince
mashi.shi kuma xai jira har ta gama
makarantanta. ahj ya katseshi ta hanyan daga
mai hannu,ibrahin kaidai sheda ne bewan bana
haka, kuma ba a haka dani ko?yace auran yata fa
kakeyi,ka san tsarina.ibrahinyace na sani ahj.
yace yauwa,ina nan ban canxa ba.yace yanxu
abinda nake san ka dashi kafin na amince da
xuwan iyayan shi.ya dubu bishira yace kinasan
shi kin amince dashi? tace eh yace tashi ki tafi
angama.kai kuma inasan kashiga unguwa uku ka
binci komin labarin yaran da usilin shi.ahj ibrahin
yace angama.yace naso ace sai ta gana
karatu,dan sai anyi sa'a xata qarasa,anma hakan
xaifimin akan doguwan soyayya kafin inxo inajin
haushi.ibrahin ya miqe to ni xan tafi.ahj shima ya
yunqura xai tashi sai waya ta kama ruri dan haka
sukayi sallama anan. ummi ta shiga gida daga
makaranta take,akuyan umman bashir tagani ta
gani a gidansu tana masu barna a kicin da sauri
ta koma ta saka sakatan gidan,sannan ta
dawo.ta kama akuyan ta kaita bakin fanfo ta tara
kanta sai kuka akuyan take tayi. Umman bashir
ta jiyo daga gidanta,da sauri ta fita taxo tana
buga gidan tana mashifa.yan baqin
ciki,mahassada,yanka min akuyan xaku yi?san
ummi bata ji ba, dan gidan ba kowa. umma taje
sheka can gidansu,hta kuma tsohuwa taje
gaisuwa n mutuwa nan kusa dasu.saida taga
akuyan ta galabaita sannan ta janyo wata leda ta
daura mata a bindi,sannan ta saketa.akuyan ta
tashi da gudu tayi hanyan fita,tace shegiya gobe
kixo ki bude mana abinci kici.taje ta bude qofar
ta jiyo muryan umman bashir,dan haka sai ta cire
sakatar sannan ta dan sanmata qofan akuya tayi
waje da gudu.saboda ledar da ummi ta qulla
mata,sai take ganin kamar binta ake,dan haka ta
nausa cikin unguwa da gudu.umman bashir na
ganin akuyarta tayi fitan bindiga,sai tabi tana
cewa,ku taremin.ummi ta koma ciki tana
dariya.ita kuma umman bashir daqar ta samu aka
ruqo mata akuyan ta.aka kwance ledan taruqo ta
xuwa gida.sai masifa take, tana isowa qofar
gidan umma.
ku biyo mu cikin litaffi na 2 domin ci gaban wannan labari.😇😇😇