AZIMA DA AZIZA ( Episode 2 )


"Yauwa yar albarka hura min, Azima lafiya kuwa kika Æ™urawa garin da zamu yi tuwo ido?" murmushi ta yi ta ce 
"Lafiya lau Hajja" girgiza kai Hajja ta yi ta duÆ™a ta shige bukka, ita kuma Aziza Hajja na shiga bukka ta rufe idonta ta rintse nan idon ya dawo ja, bakinta ta buÉ—e ta fiddo da turirin ta hura a murhu nan kuwa ya kama da wuta, Azima kuwa wajan garin ta je ta bude bakin tana shirin zuba dafi sai ga sallamar Baffa, da sauri ta mai da harshenta, amsa sallamar Baffan suka yi tare yi masa sannu da dawowa ya amsa, fitowa Hajja ta yi,ita ma ta ma sa sannu da dawowa tare da shinfiÉ—a masa tabarman kaba, ya zauna, Aziza ta É—iba masa ruwa ta kawo masa, sannan suka zauna dukkansu. 
Sai da Baffa ya sha ruwan sannan ya saki ajiyar zuciya, cikin fulatanci Hajja ta ce 
"Baffan Azima da Aziza lafiya kuwa?" 
 
"Ina kuwa lafiya, wannan alk'arya ya kafu tsawon shekaru sama da hamsin, anyi gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma a yanzu bala'in da yake tunkaro wannan alk'arya ya yi yawa, ina wannan shahararren mai kama macizai din nan, Ilu Mai Macizai?" Hajja ta ce 
"Eh na ganesa,waye bai san Ilu mai Macizai ba" 
"To shi ma an kashesa yau" salati Hajja ta sa tana tafa hannu ta ce 
"Hande in bone ni Jamila, yanzu shi ma Ilu mai macizai an kashesa?" 
 
"Eh har ma anyi masa jana'iza an binnesa, ga shi duk macizan da ake kamawa babu wanda bakinsa ya yi dai-dai da saran da ake samu, ga shi yanzu har zargi ya fara shiga tsakanin mutane da mutane, yanzu haka mai gari ya yiwa Jarman Macizai aike da wasiÆ™a,kin ganesa?" 
 
Hajja ta riÆ™e hab'a alaman tunani ta ce 
"Jarman Macizai ba wannan na yankin al'karyan jimo ba?" 
 
Baffa ya ce 
"Eh shi dai, ya ma amsa da gobe zai zo, zai taho da ruwan wani magani wanda za a ba wa kowa ya sha wanda hakan ne zai bayyana waye ba mutum ba a cikin al'umman yankin kwana, kin san titsiyeni aka yi a kan su Azima da Aziza, wai yarana basu abu irin na mutane, shi ne za ayi wannan gwajin" wani firgita Azima har ma da Azizan suka yi, suka kalli juna, ba tare da iyayensu sun san halin da suke ciki ba,tuni idon Azima ya kara komawa blue sosai, nan ta kalli fatar jikinta ta ga ta fara zama blue da sauri ta miÆ™e ta shige bukka, ita ma Azizan tashi ta yi, Hajja ta ce 
"Dan kawai yara basu mu'amala da kowa, sannan idonsu ba baÆ™i ba shikenan sai a saka mun yara a gaba?" Baffa ya ce 
"Amma kin san dai har da maganar aurar dasu, bisa al'ada ta wannan yanki namu yara da sun shekara 11 ake aurar dasu, yanzu kuma su Azima da Aziza su na da shekara 15 kin ga kuwa dole a saka musu ido mun Æ™i aurar dasu, ga shi kullum ArÉ—o sai ya min magana" tabe baki Hajja ta yi ta ce 
"Allah ya kyauta amma ai aure lokaci ne" ta miÆ™e taje duba ruwan tuwonta. 
 
A bukka kuwa sadda Azima ta shiga nan kasanta ya koma macijiya har sai da ta cika bukka din, kalar fatarta ta koma blue, Aziza ce ta biyo bayanta ta ce 
"Azima ki koma dai-dai kar Hajja ta shigo ta ganki haka fa?" 
 
A hautsine Azima ta ce 
"Dole na kashe Jarman Macizai! Nayi alkawari sai na ga bayan wanda yake shirin ya san su waye mu na asali!. 
 
"Ba ki da hankali ne Azima? Jarman macizai za ki kuma kashewa? To bari kiji! Kin ga wannan kashekashen shi zai sa a gane su waye mu, dan Allah Azima karki kashesa, bana son kisan da kikeyin nan" Aziza ta faÉ—a tana bin Azima da kallo, cikin huci Azima ta ce 
"To tsammaninki me zai faru? Idan har jarman macizai ya kawo maganin gwaji dan a tabbatar da su waye ba mutane ba? Ke a tunaninki mutanen yankinmu zasu barmu a raye ne? Ina kashemu zasu yi, dan haka kafin hakan ta kasance ni nan zan kashe Jarman Macizai kuma ba ki isa ki hanani ba" Azima ta fada tana komawa mutum tare da ficewa a bukkan, tana fitowa hanyar waje ta nufa Hajja ta ce 
 "Azima ina kuma zaki je bayan baku jima da shigowa gidan ba?" kafin Azima ta yi magana Baffa ya fito daga kewaye yana fadin 
"Ban hanaku fita sakakan ba Azima? Ina za kije?" cikin in-ina da kame-kame ta ce 
"Zan duba abu na ne a nan waje" Baffa ya ce 
"Ba za ki duba ba koma ciki" haÉ—e rai sosai Azima ta yi tare da yiwa Baffa wani irin kallo ta koma fuuu, da kallo Baffa da Hajja suka bi Azima, jiki a sanyaye Baffa ya koma ya zauna, tunanin abunda ya faru shekara ashirin shike dawo masa kwakwalwa, kar dai ace fansar da Banju ya ce zai dawo ya daukar wa kanwarsa Bahula da kansa shine ya dawo dauka kan yaransa!? Haqiqa shima zuciyarsa ta fara yi masa saqe-saqe a kan yaransa ba cikakkun mutane bane amma baya so zarginsa ya tabbata, rintse ido ya yi yana karanto kalmar "Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!" kallonsa Hajja ta yi ta ce 
"Lafiya kuwa Baffan Azima da Aziza?" 
 
"Haqiqa Jumala ina jin tsoro!"  
"Tsoron me fa Baffan yan biyu?" 
"Inajin tsoron furucin Banju lokacin da zan kashesa maganarsa ta karshe, ko kin manta da kalman da ya ce...." Baffa bai karasa ba Hajja ta dakatar da shi 
"A'a Baffan Azima da Aziza! Karka yiwa yarana baki! Taya wa inda suka mutu shekara ashiri a ce sun dawo? Azima da Aziza dai ni na haifi yarana! Kuma ni mutane na haifa, kwata-kwata wannan maganar bai kamata ace ya fito daga bakinka ba, kai da kanka ka fara zargin yaranka to ba dole jama'ar gari ma su fara zarginsu!" Hajja ta faÉ—a cikin sosuwar rai, girgiza kai Baffa ya yi ya ce 
"Ba haka bane Jumala, amma dai jikina ya yi sanyi! Allah ya kaimu gobe jarman macizai zai zo ya warware komai" ita dai Hajja ba ta sake cewa kala ba, illa aikinta da ta ci gaba da yi, Azima kuwa tana saman bukka a macijiya tana jin maganganun Baffa, a ranta take ayyana yadda zata kawar da Baffa!. 
 
 
Washe gari tun kafin garin Allah ya waye Azima ta sulale ta fice, hanyar yankin Jimo dai-dai kan layin shigowa yankin kwana a kan wata babbar bishiya ta kwanta ta nannaÉ—e idonta sun kara komawa blue, tana jiran isowar jarman macizai, awanta kusan uku kafin ta hangosa, wani murmushi ta yi mai tattare da zallar mugunta kafin ta sauko ta koma mutum, tsayuwa ta yi bayan ya gama shigowa yankin kwana. 

Post a Comment

Merci de laissez vos commentaires.

Previous Post Next Post