Wasu daga cikin masoya sukan yi murabus daga soyayya saboda wata matsala ko ɓacin rai da suka taɓa fuskanta daga abokin soyayyarsu, ko su ce sun daina ko su ce sun haƙura da soyayya.
Wai shin faɗin haka yana maganin baƙin ciki kuwa?
Hakan yana faruwa ne kasancewar dayawa daga cikin masoya sun kasa fahimtar cewa soyayya tamkar rayuwa take, wataran ka ji daÉ—i, wataran ka ji É—aci. Ba ko da yaushe ake samun yadda ake so a rayuwa ba dole wata rana a samu akasin rayuwa.
Soyayya sa'a ce, hakanan kuma aure rabo ne. Wata takan haƙura da soyayya saboda ba ta yi sa'ar irin saurayin da take so ba.
KARANTA 👉👉👉 SIRRIN ZUCI
Wata kuma tana haƙura da soyayya ne saboda samarin da take samu ba mutanen kirki ba ne, wasu mayaudara ne wasu kuma 'yan iska ne. Wata kuma ba ta ma iya rarrabewa tsakanin mayaudara da 'yan iska kokuma waɗanda ba hakan ba, kawai dai duk waɗanda suke zuwa mata ba masu tsayar da magana ba ne, daga waɗanda ba su shirya yin aure ba sai waɗanda suka kasa tafiyar da soyayyarsu yadda za ta yi daɗi.
Haka abin yake a É“angaren samari, su ma suna fuskantar kwatankwacin hakan daga wajan 'yammatansu.
To ruwa ba ya tsami banza. Wata ƙila da akwai wasu halaye ko ɗabi'u da kake da su waɗanda ya kamata a ce ka sauya su domin su zama gyara ga matsalolin da kake cin karo da su a soyayyar ka.
Ga su kamar haka:-
1. Sakankancewa mara ma'ana da wanda kake soyayya da shi.
2. Yarda wadda ta wuce misali. Kana gani kamar masoyin ka ba zai taɓa cutar da kai ba. Shi kuma cutarwa a soyayya ba sai an yi maka da gangan ba. Wani lokaci akasi da kuskure ne suke haifar da cutuwa a so.
3. Rashin cikakkiyar yarda da masoyin wanda zai iya haifar maka da zargi a cikin zuciyar ka har ma shi masoyin ya gane cewar ba ka yarda da shi ba.
4. Ba wa masoyi damar da bai kamata ka ba shi ba a fannin furuci da mu'amala ba. Idan ka ba wa masoyi wata damar za ka ga yana furta maka magana yadda ya ga dama. A ɓangaren mata kuma idan kika ba wa saurayi damar furta miki kalamai na rashin ɗa'a wataran zai kai ga taɓa jikin ki, daga nan kuma sai akai ga abin da muke magana akai na ɓacin rai domin hakan ne yake sa idan an ci moriyar ganga sai ayi watsi da ita.
5. Ruwan ido da kuma rarraba zuciyarka gida-gida. Misali, yin soyayya da masoya daban-daban kuma kowanne zuciyarka tana sonsa. Abin da ke jawo haka kuma shi ne, barin ƙofar zuciyarka a buɗe duk wanda ya zo ya shiga.
Dukkanin waɗannan abubuwan da muka kawo suna daga cikin abin da ke sanyawa ka ga masoya suna cewa su sun gaji da soyayya saboda rashin tabbas ɗin da ke cikin ta. A dalilin haka sai su ce sun haƙura da soyayyar ma gaba ɗayanta.
To abin lura anan shi ne, idan ka ce ka haƙura da soyayya ya za ka yi da halittar so da Allah maɗaukakin sarki ya yi a cikin jikin ka. Ya za ka yi da shauƙi da sha'awar da Allah ya saka maka a ran ka. Ya za ka yi da buri da muradin zuciya na son samun abin da zai kwantar maka da hankali. Taka ce fa ba ta yi kyau ba saboda rashin dacewar da ka yi a soyayya. Wasu suna can suna jin daɗin soyayyar su.
Da akwai mutane da dama waɗanda suke da buƙatar su samu soyayyar ka amma lokaci bai kawo maka su ba sai waɗanda ba su dace da kai ba suke ta kawo kansu.
Saboda haka yin murabus a soyayya ko daina ta ko haƙura da ita ba zai yi maka maganin cin amana ko yaudarar da aka yi maka ba, haka kuma ba zai cire maka haushin da ka ji na waɗanda suka ɓata maka lokaci ba, sannan kuma ba zai dawo maka da bara-bana-ba sai dai ma ka ci gaba da ɓata wa kanka lokaci har zamani ya shuɗe da kai.
Abin da za ka yi shi ne, ka nutsu ka yi soyayyar wayewa da fahimtar rayuwa ba soyayyar holewa da burgewa ba. Ka ba wa wanda ka yaba da nutsuwa da hankalin sa dama, ku yi soyayya sai dai idan aka samu akasi wanda zai iya kai wa ga an sake faɗa wa haɗarin da aka taɓa faɗawa a baya, sai a hakura har lokacin da Allah zai sa a dace.
Sannan kuma a daina saurin yanke hanzari a soyayya.
Haƙuri da juriya yana sa a fahimci hanyar da za ta ɓulle a soyayya.
Alhamdu lillah.
A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun litinin, laraba, da juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.
Source : Muryarhausa24