Ashe dama so yana da murya kuma yakan yi magana. Wani zai yi mamaki shin ta yaya so yake magana?
KARANTA 👉👉👉 Soyayyar Gaskiya
Marubuci: Nura Nakowa
Shi sautin so ba sai da kunne kaÉ—ai ake jin shi ba. Akan iya jin sautin so a cikin zuciya da gangar jiki.
Shin, ka manta daga cikin alamomin so da akwai kallo, kunya da kuma ambato? To ashe kenan kallo da kunya duk da ba sa ɗauke da nau'in sauti amma suna tura saƙon da za a fahimci abin da ake nufi.
Wannan saƙon da suke turawa kuma, wani lokacin ya fi wanda ba ki zai furta tasiri domin shi saƙo ne da ake jin shi a cikin ruhi da zuciya.
Wani lokacin ma ɗaga hannu tsakanin masoya ko motsa kai ko motsa idanuwa da sauran sassan jiki yakan sanar wanda ake tare da shi abin da ake so ko ake da buƙata.
To mu dawo batun mu na "SAUTIN SO".
Shi sauti dai a zahirance shi ne abin da muka saba ji da kunnuwanmu.
Da za a tambayeka me ka fahimta da sautin so, cikin ƙanƙanin lokaci wani zai ce kalamai masu daɗi da masoya kan gaya wa junansu. Hakane, duk wata kalma da za ta fito daga cikin baki dole sai da sauti.
Kalaman soyayya akan iya faɗarsu ta sigogi da yawa, kamar a rubuta a takarda ko saƙon waya ko hoto mai motsi da mara motsi, da dai sauran kafofin sadarwa. To amma wanda sautin murya ke fita, wannan shi ne wanda ya fi kowanne shiga cikin zuciya da kuma kama zuciya.
Idan kuma mutum bai iya ba ko kuma bai san ta wacce sigar ake iya furta kalmar da ke ratsa zuciya ba, to lallai da akwai aiki a gabansa, domin zai yi ta yi ne amma kuma ba ya ganin tasirin sa.
Kasancewar so abu ne me daɗi, to haka ake so kalmomin sa da amon sautin sa su zamto masu daɗi, masu laushi, masu sanyi, masu zaƙi, sannan kuma masu faranta rai.
A duk lokacin da ake son a furta kalmar da ake so a sace zuciya ko kama zuciya ko a ja ra'ayin wanda ake so, to sai an kula da abubuwa kamar haka:-
KARANTA 👉👉👉 SINRRIN ZUCI
1. Tausasa murya; Banda hargagi ko É—aga murya ko kausasawa wajan furta kalamai masu kama da izza ko tilastawa.
2. Ƙanƙan dakai; misali, tunda nema kake yi to sai ka yi ƙoƙarin aikata abin da zai sa ka samu, ba kuskuren da zai sa ka rasa ba.
A yayin nema za ka iya fuskantar abin da zai saɓawa tsarin ka ko kuma wanda zai ɓata maka rai. (Idan ka maida kanka bawa, wataran za ka zama sarki).
3. Tsarkin zuciya domin samun damar furta kalamai masu tsafta; idan zuciyarka ba ta da tsarki za ta dinga ingiza ka wajan yin komai a gaggauce. Ita kuma soyayya sannu a hankali ake bin ta. Ko magana idan ana yin ta da gaggawa harÉ—ewa ta ke yi.
A hurumin soyayya ana buƙatar yin magana daki-daki kuma a-jere-a-jere.
Dalilin hakan kuma shi ne, zai ba ka damar yin amfani da hankalin ka da tunanin ka wajan sarrafa kalmomin da za su dinga fitowa daga bakin ka.
Haka kuma ana so ka yi ƙoƙari wajan sassaita muryarka ta yadda za ta yi daɗi a kunnen wanda yake jin ta.
Ka koyi yin magana da aji, sannan kuma ka zama me salo ta yadda salonka zai dinga ƙara samar maka da gurbin zama a cikin zuciyar wanda kake so. Don haka ne zai sa ka ji ana mararin a ji sautin muryarka, haka kuma za ka ga ana muradin a ganka a ko da yaushe.
Masha Allah, Alhamdu lillah. Idan ka ji daɗin kasancewa da ni, to ka sanar da 'yan uwa da abokan arziki wannan shafi domin su ma su ƙaru da rubuce-rubuce na.
Nagode da ka ba ni lokacin ka.
A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun litinin, laraba, da juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.