Wata mata ce durk'ushe a filin tsakar gidan
tana faman risgar kuka, har da shashshak'a kamar zata sume saboda tsabar kukan
da take yi, sakamakon fad'an da mijin ta yake mata, gefe d'aya kuma yaran ta ne
su biyu namiji da mace suna rungume da junan su, suna taya kan su da mahaifiyar
su kukan tausayin kansu. Tsinkar muryar mahaifin nasu naji cikin tsantsar 6acin
rai da rashin mutunci yake cewa " tun da abin haka ne zan tafi na bar muku
garin gaba d'aya, na sha fad'a miki ni bana son haihuwa kwata kwata, ban shirya
yin ta yanzu ba saboda bana son ta, ga kuma shegen bak'in talaucin da muke
ciki, amman ke kamar kaza kina haihuwa babu dad'e wa ki dad'a samun wani cikin
ni na gaji " Ya k'arasa fad'i yana wani sauke numfashi, sakamakon
hayagagar fad'an da ya gama yi cikin d'aga murya da tsawa, hararar matar tashi
yake da 'ya'yan nashi, zuciyar shi cike da mugun tsanar su, ji yake kamar ya
shak'e su, su mutu ko ya huta da ganin su. Cikin shashshak'ar kuka matar tace
"Kayi hak'uri maigida, ni kaina ba ni na bawa kaina haihuwar ba, Allah ne
ya bani su taya zan butulce mishi wajen zubar da cikin da ba shege ba ne, ka
tuna haihuwa rahma ce wasu da kud'in su nema suke basu samu ba, amman kai da
Allah ya bawa kyauta kana neman butulce mishi" Ko gama rufe bakin ta bata
yi ba ya d'auke ta da wani azababban mari har guda biyu bisa kyakkyawar fuskar
ta, sake durk'ushe wa tayi tana rik'e da fuskar ta inda ya mare ta, hawaye ne
kawai yake zuba a idanun ta. Nuna ta yayi da d'an yatsan shi, cikin masifa yace
"bana buk'atar jin shawarar ki ko wa'azin ki, idan baki bi maganar da na
fad'a miki na ki zubar da wannan cikin ba, to wallahi zan bar garin don ban
shirya rainon 'ya'ya ba, naji ma da uban talaucin da ya dame ni" Yana gama
fad'in haka ya juyo kan yaran, tsawa ya kwantsama musu ba shiri suka shige
d'akin uwar ta su da gudu, jikin su na 6ari na tsoron mahaifin nasu. Tsaki yaja
tare da cewa "shegun 'ya'ya da munafurcin tsiya da sun ga uwar su na kuka,
su ma zasu fara kukan 'yan iska kawai " Yana k'arasa fad'in haka ya sake
makawa matar tashi harara tare da jan tsaki ya kad'a rigar shi ya fice fuuuu a
fusace kamar ya hantsila saboda sauri. A hankali yaran suka d'aga labulen
d'akin suna lek'en ko mahaifin nasu ya tafi, saboda jin shirun da suka ji,
ganin ya fita ne yasa su fito wa da sauri suka nufi inda mahaifiyar su take
tsugunne tana kukan nata. Rungume ta suka yi suna rarrashin ta da tayi hak'uri
ta daina kuka, daman sune masu rarrashin nata idan uban nasu ya gama yi mata
rashin mutunci. Dak'yar ta iya mik'e wa tsaye suka shiga cikin d'aki, zama suka
yi akan tsohuwar tabarmar su wadda ke shimfid'e a k'asa, kallon yaran nata tayi
cikin matuk'ar tsantsar kaunar su tare da mugun tausayin su, ta kamo hannun su
ta had'a waje d'aya tare da bud'e bakin ta tace "Aliyu ga amanar Suhaima
nan ko da bayan rai na ina son ka kular min da ita, bana son tayi kukan
maraicin na, ina son ku tsaya tsayin daka ku nemi ilimi saboda inganta rayuwar
ku ko da bana raye, ina son mahaifin ku yayi alfahari da ku a gaba, ku kasance
cikin yi wa mahaifin ku biyayya a duk abin da yace muku, ku cigaba da addu'a
watarana sai labari komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba." Cikin kuka
Aliyu yace " Umma ki daina furta cewa zaki mutu ki bar mu, zamu rayu da ke
Umma insha Allah, kuma zan rik'e k'anwa ta da kyau zan kula ta da ita Umma duk
wani kyautata wa da bata farin ciki zan bawa Suhaima a cikin rayuwar ta."
Ya k'arasa fad'i hawaye na zuba a idanun shi, cikin zuciyar shi tsanar mahaifin
shi taf a ciki, Suhaima da bani wayo ne da ita ba sosai, kallon su kawai take
tana kuka. Nan Umma ta janyo Suhaima jikin ta, rarrashin ta take har ta yi
shiru sai sauke ajiyar zuciya da take, kafin kuma ta bud'e baki tace "Umma
ni yunwa na ke ji." Umma kallon Aliyu take shima kallon Umman yake, cikin
zuciyar su suna tunanin me zasu bawa Suhaima a yanzu taci, don basu da komai a
gidan daman wani lokacin Aliyu ne yake fita yin 'yar sana'a ta k'arfi ya nemo
musu abin da zasu ci, idan kuwa ta uban nasu ne kuwa gwara su mutu da yunwa
akan ya basu abin da zasu ci. Gaba d'aya ba wanda yayi k'arfin halin bawa
Suhaima amsa, jin haka ya sanya ta fashe da kuka don ko karya wa basu yi ba
gashi yanzu azahar tana kok'arin yi, cikin rarrashi Aliyu ya janyo hannun ta
yana goge mata hawayen fuskar ta yace "yi hak'uri 'yar k'anwa ta yanzu zan
fita na samo miki abin da zaki ci, amman kada kiyi wa Umma kuka kin ji "
Gid'a kanta tayi tana mai had'iye kukan nata, da sauri Aliyu ya fita daga
d'akin, yayin da Umman ta bishi da kallon tausayi, yaron da bai fi ace yana
k'ark'arshin kulawar iyayen shi ba amman shine yake kula da kanshi, mahaifiyar
da k'anwar shi, saboda rashin dace da samun managarcin uba a gare su. Tun
Suhaima na jiran Aliyu har bacci yayi awon gaba da ita a jikin Umma tana mai
tsotsan 'yan yatsun ta a bakin ta, sai da bacci yayi k'arfi sannan Umma tayi mata
shimfid'a ta kwantar da ita. Tashi tayi ta fito zuwa tsakar gidan tsintsinya ta
d'auka ta laushi ta fara share filin tsakar gidan, tana yin sharar idanun ta na
zubar hawayen tausayin kansu, wani 6angare na cikin zuciyar ta addu'a take yi
tare da godewa Allah a halin da ta tsinci kanta a ciki, k'addarar tace ta auren
wannan mugun mijin nata mara tausayi, mai butulce wa Allah da baiwar 'ya'ya
biyu da ya bashi ga cikin na uku a jikin ta. Tun da Aliyu ya fita bai dawo
gidan ba sai daf da mangarib, hannun shi rik'e da 'yar k'aramar leda bak'a,
Suhaima na ganin shi ta mik'e da gudu ta k'arasa inda yake tare da kar6ar ledar
hannun shi tana duba wa. Garin kwaki ne a ciki sai k'ullin sugar, kallon shi
tayi fuskar ta d'auke da murmishi tace "Yaya mun gode Allah yasa ka samu
sana'a kana samun kud'i kamar yanda Yayan k'awata yake aiki yana samun kud'i
yana siyo musu abin dad'i " Cikin murmishi ya shafa kanta tare da cewa
"Amin 'yar k'anwa ta ki cigaba da yiwa Yayan ki addu'a da Umman ki ."
"Toh Yaya ina yi kullum idan nayi sallah, amman bazan yiwa baba ba tun da
shi mugu ne yana dukan Umman mu, kuma yana zagin mu da dukan mu kullum, nima na
tsane shi kamar yanda yace baya son mu ya tsane m........ " Kafin ta
k'arasa fad'in maganar taji an zabga mata wani wawan mari wanda yasa ta
hantsila k'asa, ledar garin kwakin ta baje a k'asa ta tarwatse cikin dandaryar
k'asar tsakar gidan. Ashe basu ankara da shigowar baban nasu ba gidan, yaji
abin da Suhaima ta fad'a shine yayi mata wannan marin da ko babba aka yiwa sai
haka, cikin rashin imani ya kama Suhaima ya hau dukan ta kamar Allah ya aiko
shi, Umma tana d'aki idar da sallahr mangarib d'in da tayi kenan tana sauri ta
fito don ta jawa Suhaima kunne ta daina wad'annan maganganun, don lokacin da
dawowar uban su gida yayi, sai kawai taji saukar dukan da yake yiwa Suhaima
runtse idon ta tayi da k'arfi hawaye na fita a cikin su tana mai addu'ar Allah
yasa kada yayi mata bugun da zai illata ta. Yana dukan ta cikin fushi yana cewa
"shegiya tsinanniya daman ni ai ba son ku nake ba, da zaki ce baza ki min
addu'a ba sai uwar ki da Yayan ki, na tsane ku bazan ta6a kaunar ku 'yan iska
matsiyata " Cikin kuka Aliyu yace "Don Allah Baba kayi hak'uri ka dai
na dukan ta, ka ga Suhaima yarinya ce k'arama ba zata jure dukan nan ba "
Sakin Suhaima yayi yana haki kamar wanda yake jibgar k'atu, harara ya dalla wa
Aliyu tare da cewa "Don uwar ka ni zaka fad'a wa gaskiya koh ?"

Episode 2
ReplyDelete