Yana kan tafiya akan dokinsa a hankali ya hangi budurwa tsaye a hanyarsa,magana ya hau mata amma shuru, tana tsaye da lullubi, saukowa ya yi a kan dokin ya tunkaro inda take tsaye, sai da ya zo kusa da ita kafin ya ce
" MUTUM KO ALJAN!?"
Murmushi ta yi tana lankwasa harshe ta ce
" RUWA BIYU!" sannan ta juyo ta yaye mayafin da ta lullube jikinta ta jefar, jarman macizai na ganin idonta ya yi saurin ja da baya, dariya Azima ta sheqe da shi ta ce
"Na ga bai kamata ace kasha wahala ba wajan zuwa gwajin wanene wanda ba mutum ba a wannan yankin! Gani na zo da kaina dan dakatar da kai! Ba zaka shige ba sannan ba zaka koma ba!" da sauri jarman macizai ya yi baya dan dauko kayan aikinsa tsalle daya Azima ta yi ta zama macijiya ta cakume jarman macizai nan suka hau kokawa, duk yadda yaso kwace kansa daga hannun Azima ya kasa, daga karshe ta rufesa da sara, sosai ta yi masa jina-jina sai da ta ga ya daina mutsu-mutsu sannan ta sakesa ta sulale ta yi hanyar rafin jimulo, tana isa rafin ta hau kyalkyala dariya nan ta zube kusa da rafin.
A cikin unguwa kuwa ana nan ana jiran isowar jarman macizai, tun ana sa ran ganinsa takwas har goma, inda a karshen mai unguwa ya ce aje a duba ko lafiya a binciki hanya aka tura mutum uku.
Ai kuwa can suka gano gawar jarman macizai a yashe cikin jini, cikin tashin hankali suka juya da mugun gudu suka koma suka sanar da jama'ar gari an kashe jarman macizai.
Fadin tashin hankalin da mai unguwa da jama'ar gari suka shiga b'ata lokaci ne.
Fitowa Aziza ta yi daga bukka dan tun sadda taji motsin yar uwarta jikin dare kafin garin Allah ya wayejikinta ya bata ta tafi kashe jarman macizai, abunda yasa bata yi yunkurin bin bayanta ta dakatar da ita ba sabida tasan dole Hajja da Baffa su leƙo duba lafiyarsu, tana fitowa dauke da murmushi a fuskarta Hajja ta ce
"Aziza ke kin tashi? Azima ta farka ta yi sallah kuwa?" tsilli-tsilli da ido Aziza ta fara kafin ta ce
"Eh Hajja ta tashi ta yi har ma ta fita wai ta je rafin jimulo" Aziza ta karasa maganar da in-ina sabida da asuba da Hajja ta shigo tada su kara Aziza ta jera kusa da ita ta yadda zata ga kamar Azima ce ke bacci, dan lokacin da Azima ta fita Aziza ta ji motsinta tsoron kar su fita duka a gane yasa Aziza hakura ta kwanta, dan Baffa kunnuwansa akwai saurin jiyo abu.
Kallon Aziza da kyau Hajja ta yi kafin ta ce
"Me ku ke zuwa yi kullum ne a rafin jimulo?"
"Ba komai Hajja kawai rafin akwai dadi ne, ga iska mai dadi, Hajja kin manta sadda kike kai mu muyi wasa?" murmushi Hajja ta yi ta ce
"Eh na tuna, yanzu dai je ki kirawo Azima ku zo kuci abinci"
"To Hajja, Baffa ya fita ne?" Aziza ta tambayi Hajja kamar bata san Baffan ya fita ba, Hajja ta ce
"Eh ya fita kin san ai jiya yace yau Jarman macizai zai zo, yace min idan yazo zai zo ya kiramu muje gabadaya ayi gwaji" Aziza ta jinjina kai tana fadin "to Hajja bari naje na kira Azima kafin Baffa ya dawo"
"To a dawo lafiya,ki tabbatar kinyi lullube da kyau fa"
"To Hajja" Aziza ta fada tana ficewa jiki a sanyaye, tana fita da gudu ta yanki rafi inda tasan Azima ba zata wuce can ba.
Tana zuwa ta sameta kwance a kusa da rafi.
Hannnu tasa ta janyota ta ce
"Kin kashesa ko Azima? Na ce kin kashesa ko!?" dariya ta kyalkyala cikin amo marar dadin sauraro ta ce
"Ai na gaya miki Aziza sai na kashesa!"
Rike kai Aziza ta yi ta ce
"Me kika so ki zama ne kam Azima?"
"Bana son ganin zaman lafiya a wannan yankin! Na fi so ayi ta b'arin jini! Ina so na haɗa maƙotan yankunan nan faɗa, duk wani mai kama macizai wanda za a yi masa aike ya zo yankin nan sai na kashesa! Kin ga daga nan za a fara yaƙi tsakanin yankuna da yankuna, sannan dama akwai y'ar tsama tsakanin yankin kwana da yankin tudu da kuma yankin Ja'i nasan kuma dole mai unguwa zai bukaci taimakonsu, duk wanda aka turo ni kuma zan kashesa! Na tabbata daga lokacin zaman lafiya ya kare, Baffa shine jarumi na farko a wannan yankin wanda da shi aka yi gwagwarmaya kinga kuwa ba mamaki a wajan yaƙin a kashesa!"
Zaro ido Aziza ta yi tana kallon Azima kafin ta ce
"Na rasa dalilinki na son ganin bayan Baffa! A yadda na fahimceki, ke ba ki ƙi kowa ya mutu ke ki rayu ba, idan kika samu dama na tabbata za ki kashe Baffa"dariya Azima ta kyalkyale da shi tana kewaye wajan kafin ta koma ta haɗe rai sosai ta ce
" AI BA YAU BANE KAWAI NA SHA GWADA HAKAN!ko a yanzu na samu sarari sai na kashe Baffa! Ko kin manta na sha yunkurin kashesa!? Lokuta da yawa ke ce kika katse min burikana! Ga shi ke ban san ya zanyi dake ba! Ke ta biyu na ce! Ba zan iya kasheki ba! Sabida duk muguntar gubana naki yafi nawa! Kuma ina sonki yar uwata! Da ace nike da karfin dafin da kike da shi da na jima da shafe wannan yankin kakaf dinta!" Azima ta fada tana daga hannuwanta sama.