Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa

 BURINA NA ZAMA MAI SUKUNI

Burinka kenan? To ya kamata ka sa idon lura sosai ka gane: Idan kana aikin gwamnati ne wanda ta hanyarsa ce kake samun kuÉ—i masu É—imbin yawa, kamar dai É—an siyasan da aka buÉ—a masa ya sami wani babban matsayi, kuÉ—i na zuwa masa ta ko'ina, wannan ba a la'akari da shi a matsayin mai tabbataccen kuÉ—i, matsayinsa daidai da wanda mahaifinsa ya rasu ne ya bar shi da tarin dukiya mai É—umbin yawa, kuÉ—in na zube kuma ana ganin cewa nasa ne, a zahiri ba haka abin yake ba.



KARANTA ðŸ‘‰ðŸ‘‰ðŸ‘‰ ABUBUWA 4 DAKE BATA SOYAYYA


Akwai wata 'yar gada a tsakiya, tabbas sun rabu da mahallinsu na asali zuwa wurinsa, shi kuma dole ya yi aiki don samar musu da mahalli a wurinsa, ba shi ya sha wahalar tara su ba, don haka kashe su ta kowace hanya abu ne mai sauÆ™i a wurinsa, idan muka lura da kyau wasu kansilolin da shugabannin Æ™ananan hukumomi gami da kantomomi na madafan iko iri daban-daban da zarar sun rabu da mahallan aikinsu sai ka nemi kuÉ—in ka rasa, kwashe su aka yi ko bayar da su suka yi kyauta oho. Haka waÉ—anda suka gaji maÆ™udan kuÉ—aÉ—e daga mahaifansu idan ba dace aka yi ba bayan wasu 'yan shekaru sai ka nemi waÉ—annan kuÉ—aÉ—en ka rasa, babban dalili kuwa shi ne ba a yi wa kuÉ—aÉ—en mahalli mai kyau da za a ajiye su ba

KuÉ—i duk yadda suka kai da yawa idan É—ibar su ake yi ba Æ™arowa ba, tabbas raguwa za su yi ta yi har a neme su a rasa, wanda ya gaji dukiya mai bala'in yawa a lokaci guda, ko kuÉ—in siyasa suka riÆ™a shigo masa ta ko'ina akwai buÆ™atar ya yi tsari na yadda za su ci gaba da Æ™aruwa sosai. Wannan tsarin wani abu ne mai matuÆ™ar wahala ga wanda ba ya sana'a ko ba ÆŠan kasuwa ba, domin a wannan lokacin yana da buÆ™atar sanin makama, idan ba haka ba waÉ—anda ke zagaye da shi za su iya wawurewa ba tare da ya sani ba, tsoron faruwar hakan sai ya bar kuÉ—insa a banki yana figa kaÉ—an-kaÉ—an, an kama hanyar cinye abin da aka taskace kenan.


Kwanakin baya aka ba mu labarin wani ma'aikacin siyasa da ya sami maÆ™udan kuÉ—i da ake lissafa su da miliyoyi, ya sayi gidaje da manyan benaye na shaguna, gami da filaye a wurare daban-daban, yana da tsabar sulalla a banki, idan ka lissafa abin da zai riÆ™a samu na hayar gidajennan da shaguna kuÉ—aÉ—e ne masu yawa, za su ishe shi ya gine filayen da ke Æ™asa ya zuba 'yan haya, amma sai ya haÉ—e wasu gidajen  ya samar da irin tabkeken gidannan da shi kaÉ—ai yake ciki sai matan shaÆ™atawa da ke masa É—awafi a kowani lokaci, motar da yake hawa ta miliyoyi ce, a zagaye da shi ga 'yan ku-ci ku-ba munan a duk inda ka duba, lokacin da aikinsa ya Æ™are sai rayuwar ta canja, ya riÆ™a sayar da kadarorinsa É—aya bayan É—aya, har dai ya dawo Æ™aramin gidan da yake ciki, shi ma ya sayar da rabi.





Kai da jin wannan ka san ba a yi wa dukiyar tsarin da ya dace ba, abin da yake faruwa kenan da masu gadon dukiya su ma, iya tsare dukiyan ba tare da sanin makama ba, abu ne mai matuÆ™ar wahala, shi kuma sanin makamannan karatu ne, koda kuwa mutum ba zai shiga aji ba, bari na ba ka misali, wani shugaban 'yan kasuwa ne da ake yabonsa da riÆ™on amana da adalci, aka ba shi shawarar shiga siyasa, abokan sana'arsa suka mara masa don a Æ™arshe alfanun da zai samu zai dawo musu ne, wato dai nasu ya samu, abin da ba su sani ba shi ne kowane gida da tsarinsa da kuma irin mutanen dake cikinsa, gwaninsu na É—arewa karaga ya canja abokan tafiya, sai suka fara ganin kamar ya baÉ—a musu toka a fuska, suka fita harkarsa.


KARANTA ðŸ‘‰ðŸ‘‰ðŸ‘‰ SIRRIN ZUCI


Ya sami kuɗi tabbas, kuma dama shi ma Ɗan kasuwa ne, ko na ce sarkin kasuwan ma, amma da ya sami kudi irin waɗanda ba su yake kamawa ba a baya, sai bai yi tsarin sanin makaman riƙe su ba, ƙarshe da ya sauka ba a jima ba ya dawo cikin jama'arsa, su kuwa suka yi ta ajiye masa maganganu, ba abin da yake iya cewa, bisa waɗannan dalilai ya zama dole mu dubi masu kama kuɗaɗe da yawa a wata dama da suka samu na ɗan ƙaramin lokaci, shin za mu iya la'akari da su a matsayin waɗanda suka ci nasara a rayuwa? Amsar dai ita ce "A'a!" To idan sun ajiye waɗannan maƙudan kuɗaɗen a banki me zai sa ba za mu yi la'akari da su a matsayin masu cin nasarar ba? Amsar dai ita ce sai sun mayar da kuɗin ya zama rainonsu tukun.


Wato su juya kuÉ—aÉ—en ta wata hanya yadda za su dawo da riba, ko kuma su nunku a sanadiyyar ribar da aka samu, ya zama an yi musu wani tsari mai Æ™arfi wanda za su riÆ™a Æ™aruwa ba Æ™arewa ba. A wannan matsayi ko mutum ya rabu da aikinsa ba za a iya ganin wani canji mai girma ba, kuÉ—in sun zauna kenan, in ma gado ya yi, ya sami nasarar juya kuÉ—in gwargwadon sanin makaman da ya yi, sai dai a ga kuÉ—aÉ—en na Æ™aruwa ba wai Æ™arewa ba, idan muka lura da duk bayanan sama, za mu gane cewa rashin tabbataccen tsari na Æ™aruwar kuÉ—i shi ne yake sa shi ya Æ™are


Na sami labarin wani kansila da ya yi ta yi wa wani babban mutum alkhairi kan sharaÉ—in idan ya sauka zai samar masa aiki, na ce ya san abin da yake yi, wani kuwa ya faÉ—aÉ—a sana'ar gidansu ne, ya yi ofis wanda zai riÆ™a zama idan ya sauka ya ci gaba da sa ido, shi ma ya yi Æ™oÆ™ari gaskiya. Wani da ya yi gadon maÆ™udan kuÉ—i bai canja komai na rayuwarsa ba, sai ya koyo sana'ar mahaifin ya ci gaba da ita, yanzu haka ana ganin kamar ya fi shi kuÉ—i, na ce da a ce ya sayi Æ™aton gida, ya canja mota da abokai, ya auro irin jajayen matannan, da wani Turancin ake yi ba wannan ba.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

Post a Comment

Merci de laissez vos commentaires.

Previous Post Next Post