KAFIN YA AURE TA
Menene ne ya É“ata miki rai?
Ba ki da lafiya ne naga kin yi shiru?
Wallahi idan na gan ki acikin É“acin rai, ni ma raina É“aci yake yi.
Kin san yadda nake son ki kuwa? Duk duniya babu wata 'ya mace da nake so kamar ki.
Damuwarki damuwa tace, ni fa bazan iya rayuwa ba sai da ke.
BAYAN AN YI AURE
Ke kaÉ—ai ki dinga É“ata rai saboda munafurci.
Daga anyi magana ki ƙago rashin lafiyar ƙarya, aikin banza!!
Kin zo kin yi shiru, kina wani É“ata ran banza.
Ke kaÉ—ai za ki sha damuwarki.
Idan na gan ki cikin É“acin rai, haushi kike bani.
Ba fa ke kaÉ—ai ce mace a duniya ba, kuma ko babu ke ba wani abu da zai É—aga mini hankali.
Shin mai ya sa muke wulaƙanta mata bayan aure?
Mai yasa idan muka aure su duk wani kulawa da nuna damuwa muna daina nuna masu?
Ta aminta da kai saboda yadda ka nuna mata ko babu kowa a duniya za ka riƙe ta tamkar ƙanwar ka ta jini, kuma ka biya mata duk wani buƙatun ta idan ya tashi.
Tabar gidan su saboda kai.
Tabar iyayen ta saboda kai.
Tabar garin su saboda kai.
Ta bi ka duk inda Allah ya hore maka, ku zauna ku yi rayuwa tare.
Duk wani nau'in abun jin daÉ—i, iyayen ta su na mata goma sha biyu, amma haka ta bari ta bi ka.
Shin mai yasa ba za ka iya kare mata haƙƙin ta? Ka biya mata buƙatun ta ba.
Daman duk kalaman da kake gaya mata ƙarya ce, da yaudara.
Ta ya ya mata ba za su dinga zagin maza jam'i ba?
Ya ku 'yan uwa na maza, wannan ba É—abi'ar da ya dace da miji nagari bace.
Allah ya bamu ikon kyautatawa abokan rayuwar mu. Wanda suke tare Allah ya basu haƙurin zama da juna da kuma yin biyayya ga ko wanne ɓangare, mu kuma 'yan baya, Allah ya bamu abokan rayuwa nagari wanda za mu yi rayuwa na har abada Amin.
source : MuryarHausa24